Soyayyen dankalin turawa da kwai

Nafisa Ismail
Nafisa Ismail @Nazafat_empire
Sokoto

Saukin hadi da kuma biyan bukata. #3006

Soyayyen dankalin turawa da kwai

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Saukin hadi da kuma biyan bukata. #3006

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki fyere dankali ki wanke ki yankashi da tsawo

  2. 2

    Ki zuba a tukunya ki saka ruwa kadan, gishiri da dandano sai ki dora a wuta ya tafasa

  3. 3

    Tafasan farko se ki sauke, ki tarare ruwan

  4. 4

    Ki dora mai a wuta ki jefa albasa ki barshi yayi zafi sannan ki saka dankalin a cikin mai din ki soya daidai yanda kike bukata idan ya soyu ki cire ki sa a colander ko paper towel domin ya tsane mai

  5. 5

    Ki fasa kwai, ki yanka albasa ki sa gishiri kadan sannan ki aza pan da mai kadan ki soya kwan, idan yayi ki juya dayan gefen ki soya, idan yayi miki yanda kike so se ki cire.

  6. 6

    Ina tafasa dankalin turawa a koda yaushe idan zan soya domin shi ke hana ya lakuce, duk lokacin da zaki ci shi zaki ganshi kamar yanzu kika gama suyar.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Nafisa Ismail
Nafisa Ismail @Nazafat_empire
rannar
Sokoto
Ina sha'awar girke girke masu dandano da kara lafiya a jiki.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes