70 pieces cake (measurement, pricing and packaging)

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

musamman domin 'yan kasuwa. Mutane da dama suna yawan tambayana adadin cake da measurement, musamman ga wanda suke farkon fara kasuwancin cake. Wasu suna gudun su yi mixing yadda zai yi yawa ko kuma ya yi kadan. Wasu kuma yadda za su fitar da kudin ne yake musu wahala. Sannan kuma wasu packaging ne ke ba su iya ba. Ku biyo ni a cikin wannan recipe na cake, inda zan kawo muku komai dalla-dalla. Da kuma hakikanin measurement da zai ba ku 70 pieces na cake. Idan 100 kuke so sai ku kara. Idan ma 50 ne sai ku rage. #team6cake

70 pieces cake (measurement, pricing and packaging)

musamman domin 'yan kasuwa. Mutane da dama suna yawan tambayana adadin cake da measurement, musamman ga wanda suke farkon fara kasuwancin cake. Wasu suna gudun su yi mixing yadda zai yi yawa ko kuma ya yi kadan. Wasu kuma yadda za su fitar da kudin ne yake musu wahala. Sannan kuma wasu packaging ne ke ba su iya ba. Ku biyo ni a cikin wannan recipe na cake, inda zan kawo muku komai dalla-dalla. Da kuma hakikanin measurement da zai ba ku 70 pieces na cake. Idan 100 kuke so sai ku kara. Idan ma 50 ne sai ku rage. #team6cake

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 500 gbutter (2 simas)
  2. 6 cupsflour
  3. 2 cupsmilk
  4. 12eggs
  5. 2tea spoons baking powder
  6. 2 cupssugar
  7. 1bottle vanilla flavor
  8. 2tea spoons milk flavor
  9. Kayan aiki (instruments)
  10. Babban bowl wanda za a yi kwabi a ciki
  11. karamin bowl wanda za a fasa kwai
  12. Fork wanda za a fasa kwai
  13. spoon wanda za a ke gyara kwabin in case ya barbaje
  14. hand or standing mixer
  15. cupsPaper
  16. Cupcakes baking pan
  17. Oven
  18. cupsMeasuring

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga abubuwan bukata

  2. 2

    Ga wasu daga cikin kayan aiki

  3. 3

    Ki fasa kwai duka

  4. 4

    Sai ki zuba butter duka guda biyun a cikin baban bowl

  5. 5

    Ki zuba sugar a cikinsa

  6. 6

    Ki yi mixing on a high speed har sai ya yi farin kala

  7. 7

    Sai ki rinka zuba kwai a hankali da kadan kadan kina mixing har sai kin juye duka

  8. 8

    Ga yadda zai yi nan

  9. 9

    Sai ki zuba madara ita ma da kadan kadan har ki juye duka. Ki ajje a gefe idan kin gama wannan.

  10. 10

    Ki zuba baking powder da milk flavor a cikin flour a wani bowl din daban. Ki yamutse sosai.

  11. 11

    Sai ki dauko wancan mixture din kina zuba flour kadan kina mixing har ki gama duka.

  12. 12

    Ki zuba vanilla flavor ki yi mixing on a low speed.

  13. 13

    Kun ga yadda kwabin ya yi kyau sosai.

  14. 14

    Ki jera paper cups a cikin pan din. Sannan ki zuzzuba cokali daya da rabi na kwabin a kowanne cup.

  15. 15

    Na saka a cikin oven. Minti goma da wutan qasa then minti biyar zuwa bakwai da wutan sama da qasa. Depends on karfin wutanku dai.

  16. 16

    Ga shi nan bayan ya gasu.

  17. 17
  18. 18
  19. 19

    Is all about team 6 challenge.😍

  20. 20

    One secret a baking cake shi ne, ina fara baking da wutan qasa. Bayan ya yi tsakiya a gasuwa sai in mayar wutan sama da qasa. Amfanin yin haka shi ne, kunna wutan sama da qasa a tare shi yake saka samanshi ya farfashe. Farawa da wutan sama kuma yana saka cake ya lokame ya qi tashi. Amma idan aka yi amfani da yadda na turo za ku same shi da kyau sosai kaman yadda na yi.

  21. 21

    Sai wurin packaging kuma na yi amfani da homemade box. Ni na hada da kaina. If baki iya ba kuma sai ki siyo a kasuwa. Ki yanka foil paper daidai girman box din. Sai ki shimfida ta a ciki.

  22. 22

    Sai ki kawo cakes din ki yi arranging da kyau. A kowane guda daya na zuba guda 35. Sannan na lika sticker mai dauke da sunana da adireshi sai kuma lambar waya. Na yi rubutu a plain sheet na yi godiya ga customers dina.

  23. 23

    Wajen pricing kuma ina fara amfani da abin da na kashe na kudi. Idan na lissafa duka sai in duba nawa ya kamata in qara yadda ba zan cuci kaina bah? Yadda kuma ba zan kwari customers dina ba? Sai in fitar kawai.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

sharhai (15)

Suwaiba Ismail muhammad
Suwaiba Ismail muhammad @cook_28954143
measurement nake so na simas sugar da egg idan inaso nai 100 pieces don Allah.

Similar Recipes