Cake mai kwakwa (coconut cake)

Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
Kaduna

Wannan cake ne da ya sha bamban da duk sauran wasu cakes da kuka sani. Domin kuwa kina cin shi ne kai tsaye tamkar zallar kwakwa kike ci. Ga wani dandano da babu yanda za a misalta shi har sai idan an ci an ji yanda yake ne. Jiya wata customer ta zo tana so na mata cake. Na tambaye ta wanda take so sai ta ce ta bar ni da zabi. Kawai dai mai dadi sosai. Shi ne na shawarceta da cake mai kwakwa. Ta zo ta karba kuma ta kira ni tana ta godiya. Har ta ce ma za ta sake dawowa na mata irinsa. Wannan measurement din zai yi kimanin guda 40 zuwa 45. #team6cake

Cake mai kwakwa (coconut cake)

Wannan cake ne da ya sha bamban da duk sauran wasu cakes da kuka sani. Domin kuwa kina cin shi ne kai tsaye tamkar zallar kwakwa kike ci. Ga wani dandano da babu yanda za a misalta shi har sai idan an ci an ji yanda yake ne. Jiya wata customer ta zo tana so na mata cake. Na tambaye ta wanda take so sai ta ce ta bar ni da zabi. Kawai dai mai dadi sosai. Shi ne na shawarceta da cake mai kwakwa. Ta zo ta karba kuma ta kira ni tana ta godiya. Har ta ce ma za ta sake dawowa na mata irinsa. Wannan measurement din zai yi kimanin guda 40 zuwa 45. #team6cake

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 3kofi flour
  2. 1kofi sugar
  3. 1kofi coconut milk
  4. 6kwai
  5. g+1/4 cup butter 250
  6. Coconut flakes (kwakumeti) yanda zai yi
  7. Vanilla flavor 1 tea spoon
  8. Coconut flavor 1 tea spoon
  9. Baking powder 1 tea spoon
  10. Milk flavor 1 tea spoon
  11. Coconut flakes
  12. Kwakwa guda daya
  13. sugar 1/2 kofi
  14. Flavor (optional)
  15. 1tablespoon oil

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki fara da hada coconut flakes din. Ki gurza kwakwa daidai girman da kike so.

  2. 2

    Sai ki zuba sugar a ciki ki jujjuya

  3. 3

    Sai ki zuba mai a pan ki baje shi a kaskon duka ya game ko'ina. Sai ki zuba kwakwar

  4. 4

    Ki saka wuta kadan. A hankali kina jujjuya shi har ya canza kala ya koma golden brown.

  5. 5

    Sai ki kwashe. Ki juye a tray ya sha iska.

  6. 6

    Shi ke nan kin hada coconut flakes da aka fi sani da kwakumeti.

  7. 7

    Ga abubuwan bukata idan za a hada cake din

  8. 8

    Ki zuba flour a babban bowl sai ki zuba baking powder da milk flavor

  9. 9

    Ki zuba butter a wani bowl daban. Ki zuba sugar a ciki

  10. 10

    Ki yi mixing sosai har sai sugar ya gama narkewa

  11. 11

    Sai ki zo da kadan kadan kina zuba kwai kina mixing

  12. 12

    Ga shi nan yanda zai yi.

  13. 13

    Sai ki zuba coconut milk. (na yi amfani da homemade. Na wanke kwakwa na fere bakin bayanta. Sai na gurza na saka a blender na markada. Sannan na tace. Shi ke nan.)

  14. 14

    A zuba coconut flavor da vanilla flavor

  15. 15

    Sai a hankali kina zuba flour kina mixing

  16. 16

    Har sai kin ganshi ya yi haka.

  17. 17

    Sai ki jera paper cups a pan

  18. 18

    Ki yi amfani da 1/4 cup kina diban batter din kina zubawa a ciki

  19. 19

    Sai ki zuzzuba coconut flakes da kika yi a kai.

  20. 20

    Ki saka a oven ki kunna wutan qasa. Idan ya yi kaman tsakiya a gasuwa sai ki mayar da shi wutan sama da qasa. Amma ki kula sosai kar ya cika golden don kar kwakwar duk ta qone.

  21. 21

    Ga shi nan bayan na gama

  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26

    Bayan na yi packaging

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Princess Amrah
Princess Amrah @Amrahskitchen98
rannar
Kaduna
I absolutely love cooking. I can merrily state that my kitchen is my playground in every sense! My mother has always been a wonderful cook, and I feel she is my inspiration.
Kara karantawa

Similar Recipes