*my first recipe contest* yam balls da kunun aya

Fadique Kitchen
Fadique Kitchen @fadique_kitchen
Kaduna State Nigeria
Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Abubuwan da ake buka wurin yin yam balls
  2. Doya
  3. Attarugu
  4. Tattasai
  5. Albasa
  6. Kwai
  7. Nama
  8. Kayan dandano
  9. Man gyada

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaka sami doya ka fere ta. Idan ka gama zaka yanka shi kananu. Saika wanke ka zuba ruwa tukunya sai ka dora kan wuta sai ka zuba doyan ciki. Saika zuba maggi da gishiri. Saika rufe ka barshi ya dahu ya danyi taushi. Sai ka sauke ka tsane ruwan.

  2. 2

    Daga nan zaka dauko su attarugu tattasai da albasa zaka wanke su sai ka markada su sama sama ko ka jajjaga su. Idan ka gama zaka dora tukunya kan wuta sai ka zuba man gyada kadan. Saika zuba kayan jajjagen ka zuba kayan dandano sai ka soya kadan

  3. 3

    Daga nan zaka dauko doyan ka da kariga ka dafa.zaka zuba shi cikin ruba ka saka hannu ka murje shi ko ka saka cikin turmi ka daka.

  4. 4

    Daga nan zaka dauko jajjagen ka da riga kadan soya. Zaka zuba shi cikin murzazjen doyan ka. Saika juya ya hade sosai.zaka iya sakawa baki kaji idan kayan dandano sunyi. Idan ba suyi ba zaka iya karawa dai dai. Sai ka juya ya hade.

  5. 5

    Daga nan zaka dun kula hadin doyan yayi kaman ball. Zaka yiwa doyan dakan shi haka.

  6. 6

    Daga nan zaka fasa kwai cikin kwano kana saka dunkulen doyan cikin ruwan kwai kana sawa cikin man gyada mai zafi. Sai ka soya har yayi golden brown saika kwashe

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fadique Kitchen
Fadique Kitchen @fadique_kitchen
on
Kaduna State Nigeria

Similar Recipes