Miyar Ofada (Sauce)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

To nidai ban ma san sunan wannan miyar ba da dadin ta ma baa magana
Munje Abuja recently aysha Adamawa ta yi mana wannan miyar ta yan gayu me dadi shine na ce nima bari in gwada amma tawa bata kai yajin ta aisha ba 😅

Miyar Ofada (Sauce)

To nidai ban ma san sunan wannan miyar ba da dadin ta ma baa magana
Munje Abuja recently aysha Adamawa ta yi mana wannan miyar ta yan gayu me dadi shine na ce nima bari in gwada amma tawa bata kai yajin ta aisha ba 😅

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1hour
2 yawan abinchi
  1. 10Tarugu
  2. 5Shambo
  3. 2Tattassai
  4. 2Albasa
  5. 7Tafarnuwa
  6. 4Maggi
  7. 2Kwai daffafe
  8. Daddawa chokali 1
  9. Man ja rabin kofi
  10. Man gyada rabin kofi
  11. Curry kadan
  12. Soyayyen nama
  13. Ganda daffaffa
  14. Busasshen kifi

Umarnin dafa abinci

1hour
  1. 1

    Zaki jajjaga kayan miyar ki
    Tatugu tattassai albasa tafarnuwa da shambo

  2. 2

    Ki jika kifin ki ki dafa ganda
    Daman naman ki soyayene

  3. 3

    Ki aza man ja da man gyada tare se ki zuba daddawar yarbawa kafin ya yi zafi sosai
    Kita juyawa se ki zuba jajagenki

  4. 4

    Idan sun soyu se ki zuba maggi ganda soyyayen nama da kifi ki zuba ruwa kadan se ki rufe ya dan kara dahuwA

  5. 5

    Da sun dan kara dahuwa se ki saka kwai ki bada mintuna kadan se ki kwashe

  6. 6

    Masha Allah sauce dinki ta kammalla se ki nemi shinkafar ki me lafia da sobon ki me sanyi ki hada

  7. 7

    To yaron duk da bejin magana baya cikin wannnan lamarin 😉

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes