Zebra alale da miyar yaji

Wake dai wani sinadari ne na abinci mai qara lafiya(protein),San nan nayi amfani da ganyen alayyahu,shima yanada nashi sinadaren mai muhimmanci. Alale dai abinci da hausawa da yarbawa sukafi sarrafawa a gida da wajen taro. #alalerecipecontest

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki auna wake ki zuba ruwa kisa a turmi ki cashe ta dan cire bawonsa da duk wani datti.
- 2
Bayan nan ki qara wanketa dan tabbatar da komai ya fita. Saiki barta cikin ruwa ya qara minti 30.
- 3
Sai ki koma kan kayan miya da alayyahu ki gyara ki yanka ki ajiye a gefe.
- 4
Saiki zuba waken,kayan miya,tattasai,attarugu,albasa,karafish,curry,thyme,oil,ruwan zafi,tafarnuwa,kayan dandano,citta, duka ki niqesu yayi laushi sosai sosai.
- 5
Saiki qara. Kar a cika gishiri saboda Alayyahu nada sinadarin gishiri tartare dashi.
- 6
Saiki zuba Alayyahu a kwabin ki juya.
- 7
Bayan tayi laushi,Saiki dandana kiji abinda beji ba
- 8
Ki shafa mai a jiki,ki zuba qullun har kusan bakin kwanan.
- 9
Saiki saka a cikin tukunya mai ruwa dake tafasa ki rufe tukunyar harsai ta dahu.
- 10
Saiki kifa a kwanan ci,tare da miyan yaji na manja.
- 11
Saiki samu babban plastic container ko baking pan mai qusurwa 4.
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (2)