ALALA da KWAI da KIFI

Ummu Khausar Kitchen @1987kau
Wake abinci ne mai gina jiki,mutane da dama na son alala har da ahalin gida na.shiyasa nake yi.
ALALA da KWAI da KIFI
Wake abinci ne mai gina jiki,mutane da dama na son alala har da ahalin gida na.shiyasa nake yi.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki surfa wake ki wanke ki wanke kayan miyar ki a yanka albasa akai markade,
- 2
Bayan an kawo sai ki hada a zuba Mai da farin Maggi nafi amfani gaskiya dashi saboda test kuma bayasa tauri sabanin dunkule,sai ki zuba su thyme da ounga da gishiri da ki juya,sai a fasa kwai asa kifin gwangwani da albasa a yanka.
- 3
Sai ki kulla ki zuba ruwa a tukunya ya tafasa sai a tsoma a acikin ruwan a barshi ya dahu,in yayi sai a sauke abarshi ya huce ayi saving da mai da.dan yaji
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9459184










sharhai