Danbun Naman Kaza

Rahma kabir
Rahma kabir @rahmakabir
Kaduna

#Kadunastate. Danbun naman kaza, its my favorite. Akwai dadi musamman mutum yaci da dare ya kora da lipton.

Danbun Naman Kaza

#Kadunastate. Danbun naman kaza, its my favorite. Akwai dadi musamman mutum yaci da dare ya kora da lipton.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Kaza
  2. Mai
  3. Maggi
  4. Curry & spices
  5. Tarugu
  6. Garin citta

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki yanka kaza part part ki wanke ki sanya a tukunya karki sanya ruwa, ki sanya maggi, curry, spices, garin citta ki tafasa tayi luguf ruwan jikin kazar zai fito ki bari ya shanye a jikinsa.

  2. 2

    Ki kwashe a roba ki zare kashin tare da fatar kazar, ki zuba zallar tsokar a tukunya, sai ki samu tarugu ki yanka ko ji jajjaga ki zuba a ciki, ko ki wanke tarugun ki zuba a kazar, ki dauko muciya ki rinka daddakawa a hankali, za kiga tsokar yana rarrabuwa, ba a son ya daku sosai.

  3. 3

    Bayan kin gaba dakawa sai ki kara maggi da curry ki juya, ki sanya mai a tukunya ki daura a wuta, kar ki soya a kasko, in yayi zafi sosai sai ki zuba kazar da kika daka, ana so mai din ya sha kan naman, ki zauna kina yi kina juyawa.

  4. 4

    In ya soma yi zai fara kumfa sosai ya soma yin brown color, in ya karasa zai zama brown sosai, ki zuba a matsani mai ya dige, sai ki zuba a mazubi ki rufe in ya kwana biyu man ya kai kasa, sai ki sanya abin tace koko ki mace mai din shikenan sai ci.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rahma kabir
Rahma kabir @rahmakabir
on
Kaduna
I love cooking.
Read more

Comments

Similar Recipes