Shawarma sandwich

Leemah.s_cuisine
Leemah.s_cuisine @cook_18331560
Kano Nigeria

#kano. Yanada dadi ga saukin yi sosai

Shawarma sandwich

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#kano. Yanada dadi ga saukin yi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Buredi me yanka yanka (manya)
  2. Kwai
  3. Kuren tattasai
  4. Karas
  5. Bama(mayonnaise)
  6. gwangwaniKifin
  7. Attaruhu da albasa
  8. Kabeji
  9. Kayan dandanon girki
  10. Man gyada

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Xaki samu kwae dinki ya danganta da yawan wanda xakiyi, idan kaman goma xakiyi amfani da sae ki dafa guda biyar ki yayyan kashi kamar haka

  2. 2

    Ragowan biyar din saeki fasasu ku yanka albasa kisa maggi dinki ki kadashi kaman haka

  3. 3

    Saeki ki jajjaga attaruhun ki da albasa kokiyi giretin dinsu kaman haka

  4. 4

    Saeki dauko kifin gwangwanin ki kidaura tukunya ko kasko a wuta saeki xuba kifin a ciki kidan faffasashi da abin juyawanki, saeki xuba jajjagen attaruhunki da albasa a ciki idan yadan soyu saeki xuba daffafen kwanki a ciki ki juyasu yadan soyu, kidan zuba kayan dandano a ciki,idan Yadan soyu saeki dauko danyan kwae dinki sae kixuba kina juyawa harya soyu a ciki ya hade jikinshi, yaxama ba ruwa a ciki kaman haka.....saeki ajiyeshi a gefe

  5. 5

    Saeki yayyanka kabejin ki da koren tattasae dinki siraran yanka ki wanke kitsane shi, ki goga karas dinki shima, saeki yadesu guri daya ki saka bama dinki ki juyasu sosae kaman haka

  6. 6

    Saiki dauko biredin ki,sae kina dauka daya saeki dan shafa masa bama kadan akae amma ba dole bane, saeki debi hadin kabejinki ki xuba akan biredin ki tabbatar ko ina yasamu kaman haka

  7. 7

    Saeki dora dayan hadin naki na kifi akae shima ko ina yasamu sosae kaman haka

  8. 8

    Sae ki rufeshi da wani biredin, ki kuma maimaita yadda kikayi akae shima saeki rufeshi, xaki iyayi hawa uku ko hudu duk yadda kikeso, saeki samu kasko dinki ki ke dan diga mai ajiki kina dorawa akae,idan yadan soyu saeki juya shi amma dadewa xaeyi ba minti daya ma ya isa kin gama daya kaman haka

  9. 9

    Sae saka a plate me kyau ki rabashi biyu kaman haka....shikenan sae ci

  10. 10

    Aci lafiya.....

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Leemah.s_cuisine
Leemah.s_cuisine @cook_18331560
rannar
Kano Nigeria

sharhai

Similar Recipes