Beetroot,carrot rice with beef Kebabs(Arabian style)

Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
Kano

Ina son gwada sabbin salon girkunan labarawa,musamman shinkafa...girkunan Larabawa suna da wani sirrika na daban musamman spices dinsu suna da matukar amfani a jikin dan adam♥️💯

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

40mins
mutum 4 yawan abinchi
  1. nd half cup basmati rice(soaked) 1
  2. 1medium beetroot
  3. 2medium carrots
  4. Sweet corn
  5. Red kidney beans
  6. 1medium albasa
  7. Cardamom pods, cinnamon stick, clove's,cumin seeds,star anise
  8. Masoro da curry leaves
  9. tafarnuwaCitta da
  10. Sinadarin dandano
  11. Ruwan nama (chicken stock)
  12. Man kuli(veg oil)
  13. For the beef Kebabs
  14. Nikakken naman
  15. tafarnuwaCitta da
  16. Albasa
  17. Attaruhu ko green chilies (optional)
  18. Curry leaves
  19. Sinadarin dandano
  20. Curry,thyme da spices mix
  21. Tsinken tsire

Umarnin dafa abinci

40mins
  1. 1

    Kisa veg oil dinki a tukunya da cardamom,cinnamon,Star anise,cloves da cumin seeds ki soya sama sama....

  2. 2

    Sannan ki zuba citta,tafarnuwa da albasa kita juyawa hartayi laushi....

  3. 3

    Sannan ki kawo shinkafarki da kika Jika na tsahon 20mins kika wanke Ki zuba a ciki kijuya....

  4. 4

    Ki zuba ruwan nama(Chicken stock)da tafasshen ruwa daedae yadda zae dafa miki shinkafarki kisa sinadarin dandano....

  5. 5

    Kisa curry leaves ki juya komae y hade,ki rufe bakin tukunyar sosae,ki barta ta dahu for 15mins...

  6. 6

    Idan ruwan y zama saura kadan y tsotse saeki saka carrots,beetroot da kika gogah a gefe-gefe kamar hka...sannnan kisa red kidney beans da sweet corn,ki rufe tukunyar ki rage wuta ta turarah for 5mins.

  7. 7

    Yadda zaki hada beef Kebabs;kisa mincemeat,ginger,garlic da curry leaves a blender ki kara nikasu sosae,idan kinason yaji zaki iya saka attaruhu Ko green chilies,ki juye a bowl kisa sinadarin dandano dana kamshi Ki juya sosae komae y hade.sannan Ki dinga diba kina mulmulawa a jikin tsinken da dan fadi Ki shafa oil jikin pan ki gasa both sides din har yayi.

  8. 8

    Bayan ta tura saeki juya zakiga ta baki color din nan mae kyau,Tom shikenan mun gama beetroot rice dinmu🥰

  9. 9

    Alhamdulillah done 😋😋💯

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Wanda aka rubuta daga

Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
rannar
Kano

Similar Recipes

More Recommended Recipes