Arabian carrot rice

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

#FPPC ina tunanin mezandafa sai nayi tunanin dafa shinkafa kuma banida kayan lambu sai karas kadai nake dashi. Shiyasa nace bari nayi carrot rice sai nasarrafashi tanan kuma nasaka inibi aciki

Arabian carrot rice

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

#FPPC ina tunanin mezandafa sai nayi tunanin dafa shinkafa kuma banida kayan lambu sai karas kadai nake dashi. Shiyasa nace bari nayi carrot rice sai nasarrafashi tanan kuma nasaka inibi aciki

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Attarugu
  3. Mai
  4. Albasa
  5. Inibi
  6. Bey lef
  7. Cinnamon stick&powder
  8. Maggi knorr
  9. Maggi dunkule
  10. Madish curry and chicken
  11. Thyme
  12. tafarnuwaCitta da
  13. Black pepper
  14. Karas manya guda biyar ko shida
  15. Onga classic

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zakiwanke shinkafa sannan kitsane kibarta tasha iska sai kidaura tukunya awuta kisa mai dayawa sannan kidauko shinkafar kixuba akai kiyita juyawa har tasoyu takoma brown. Sai kisauke kijuye a madambaci amma nakarfe sbd naroba zai narke. Bayan kinjuye sai kibari mai din yafita duka ajiki

  2. 2

    Sai kidaura tukunya a wuta kisa mai kadan sannan kizuba albasa da Cinnamon stick da beylef kibarta tadan soyu sannan kijajjaga citta da tafarnuwa kizuba kijujjuya sannan kizuba jajjagen attarugu kisake jujjuyawa

  3. 3

    Sai kizuba tafasashshen ruwa daidai wanda zai dafa miki shinkafar. sannan kidauka shinkafar kizuba akai sai ki jujjuya sannan kizuba black pepper

  4. 4

    Sannan kisa maggi ki jujjuya sai kisa curry thyme da madish da onga kijujjuya sannan kisa Cinnamon powder kijujjuya sai kirufe kibarta zuwa mintuna kadan

  5. 5

    Bayan mintuna kadan sai kiduba idan ruwan yakusan tsotsewa sai kizuba karas dinki da kika wanke sannan kika gurza da abun gurza kubewa sannan kizuba akai kijujjuya

  6. 6

    Bayan kinjujjuya sai kiwanke inibi kizuba akai kisake jujjuyawa sai kirufe idan yanuna sai kisauke shikenan kingama

  7. 7

    Zaki iya hadawa da duk irin souce dinda kikeso kici

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes