Fish rolls daga Amzee’s kitchen

Amzee’s kitchen
Amzee’s kitchen @zainabkabir52
kano

Yanada dadi da tea 😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 4 cupsFulawa
  2. 1 tbspnYeast
  3. Salt 1 tspn
  4. 3 tbspnButter
  5. Ruwan dumi
  6. 1 tbspnSugar
  7. Kifi
  8. Attaruhu
  9. Albasa
  10. Kayan kamshi
  11. Maggi
  12. Mai
  13. tafarnuwaCitta da

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zakiyi tankade fulawa sai kisa gishiri ki juya sannan kisa sugar da yeast ki jujjuya

  2. 2

    Sannan sai kikawo ruwan dumi kizuba ki kwaba saiki kawo butter kisa ki kwaba sosai har yazama soft dough sai ki rufe ki ajiye agefe

  3. 3

    Filling Zaki wanke kifinki sosai ya fita sai ki zuba a tukunya kisa kayan kamshi da maggi da albasa sai a dora a wuta ya tafasa

  4. 4

    Bayan ya tafasa sai a kwashe acire kaya a murmusheshi

  5. 5

    Bayannan sai a dora pan a uwata a zuba mai kadan sannan a sa albasa asa citta da tafarnuwa sai asa attaruhu ajuya kamar minti biyar sai akawo kifin azuba asa black paper da curry da sauran kan kamshi

  6. 6

    Sai ayita juyawa har yayi yanda ake bukata shikenan sai a sauke a jiye

  7. 7

    Bayannan sai a dakko dogh din a gutsira kanana sannan sai adinga murzawa dogaye anasa kifi a farko sai adinga nannadewa ana ajiyewa

  8. 8

    Bayannan sai adora mai awuta idan yayi zafi sai adinga sawa ana soyawa haryayi golden brown shikenan nan sai a tsane a colander

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Amzee’s kitchen
Amzee’s kitchen @zainabkabir52
rannar
kano

sharhai

Haleema babaye
Haleema babaye @Heelamatu
Nabi wanann recipe yayi dadi sosai

Similar Recipes