Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Flour kofi
  2. Kifi
  3. Attaruhu
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Curry
  7. Thyme
  8. Baking powder
  9. Salt
  10. Butter

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaa sami flour a zuba a roba sai a kawo sugar, Salt,egg baking powder, da butter a cakuda sosai har sai komai ya hade sai a kawo ruwa mai sanyi a zuba a juya sosai har sai ya hadu sannan a fadada da rolling pin. A rufe da kitchen towel a aje a gefe.

  2. 2

    A sami kifi mai kyau a gyarashi sannan a wanke da lemon tsami ko vinegar sannan a tafasa shi. Idan ya huce sai a cire kayoyin sannan a marmasa a aje a gefe.

  3. 3

    Zaa dauko attaruhu a wanke a jajjaga, a wanke albasa da tattasai a yankasu yadda akeso sai a zuba mai a kasco kadan idan yayi zafi sai a zuba albasar a juya daga nan sai a zuba attaruhu da tattasai a juya, a zuba magi thyme, curry a juya sai a kawo marmashen kifin a zuba a yi ta juyawa har sai yayi sai a sauke.

  4. 4

    Idan ya huce sai a dauko kwababban fulawar da aka fadada a zuba hadin kifin daga gefe sai a nannada kamar tabarma anayi ana shafa ruwa jikin fulawar har a gama sai a saka wuka a rarraba, a jera a farantin gashi sai a shafa ruwan kwai a saman sannan a gasa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
ummusabeer
ummusabeer @cook_12539941
rannar
Kano
Cooking is my pride
Kara karantawa

Similar Recipes