Alale

Bint Ahmad
Bint Ahmad @Bint92
Sallari,Kano Nigeria.

#PAKNIG...RAMADAN MUBARAK 💞

Tura

Kayan aiki

50mintuna
2 yawan abinchi
  1. Wake kanana kofi 2 da rabi
  2. 3Albasa kanana
  3. 5Attarugu
  4. 1Tattasai
  5. Mangyada/Manja yanda ake bukata
  6. Kori,maggi,gishiri, yanda ake da bukata
  7. 4Kwai

Umarnin dafa abinci

50mintuna
  1. 1

    Zamu jika wake sai mu sirfa mu wanke shi idan mun cire dusar sai mu dan sa ruwa mu jika shi sannan mu zubar da ruwan,sai mu gyara albasa,attaruhu da tattasai mu wanke mu zuba a ciki akai mana nika kuma muce ai nikan da laushi(saboda idan yayi laushi alalen yafi dadi).

  2. 2

    Idan an Nika sai mu kara ruwan dumi yanda dai mukeso kaurin kullin sai mu zuba maggi,kori da gishiri da mangyada/manja sai mu jujuya.Sai mu dafa kwai mu bare mu raba biyu idan mun gama Hadin mun zuba a leda sai mu rinka daukan barin kwan muna zuba wa a leddar sai a kulle ana tsomawa a tafashashen ruwa ko wanda ya soma zafi idan aka gama sakawa a tukunya sai a datse murfin amma a yalwaraciyar tukunya zaa saka ta yadda ko ya taso bazai zube ba.

  3. 3

    Sai a barshi yayi ta dahu minti 35-40 idan ya dahu sai a sauke ana iya ci da mai da yaji ko Sauce.Iftar Mubarak

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Bint Ahmad
Bint Ahmad @Bint92
rannar
Sallari,Kano Nigeria.
For me,the kitchen is the most special room in the house.Its a place for adventure -not drudgrey,but discovery,sharing and showing off with friend's,trying new ideas.♡☆
Kara karantawa

sharhai (2)

Safiyya
Safiyya @cook_25625352
Za'a iya sa danyan kwai a qulinn

Similar Recipes