Alalan gwangwani

Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
Sokoto State

Alala na manja,wanda nayi amfani da gwangwani wajen yinta. Tayi matukar dadi hakama iyalina sunji dadinta sosai😋

Alalan gwangwani

Alala na manja,wanda nayi amfani da gwangwani wajen yinta. Tayi matukar dadi hakama iyalina sunji dadinta sosai😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake,kanana
  2. Tarugu
  3. Tattasai
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Maggi fari
  7. Onga,ja
  8. Gishiri
  9. Mai
  10. Manja,soyayye
  11. Acida
  12. Manja, soyayya
  13. Yaji
  14. Albasa,yankakka

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara wakenki,saiki da kashi acikin turmi,har bawan waken ya fita. Saiki wanke shi da kyau sosai kicire bayan. Sannan ki gyara tarugu,tattasai da albasa kisa,sai amarkadashi. Zaki iya amfani da blender kiyi blending dinshi,amma saikin jikashi kamar tsawon awa daya

  2. 2

    Bayan anmarkadashi,zaki juyeshi cikin roba mai fadi

  3. 3

    Saekisa Maggi fari,da kuma Maggi saikuma ki zuba onga ja kadan bada yawaba

  4. 4

    Sannan saiki motsa,ki jujjuya da kyau ta inda dukkanin maggin zai hade. Bayannan saiki zuba gishiri, ba'a zuba gishiri saikin fara zuba maggi sbd kada yayi yawa

  5. 5

    Saiki zuba mai kadan, sannan ki zuba manja ki motsa. Manjan da nasa yafi yawa saboda alalan manjace

  6. 6

    Zaki shafa manja acikin gwangwanin da zaki dafa alalar,idan alalar da zakiyi bata manja ceba,to zaki shafa mai akai, sannan saiki zuba kullun waken acikin gwangwanin

  7. 7

    Kisamu babbar tukunya,saiki zuba ruwa ta inda bazasu shiga cikiba idan yatafasa, sannan saiki jerasu,ki rufe tukuna yayita dahuwa. Zaki ringa dubawa idan ruwan ya kare saiki kara wasu hatta dahu

  8. 8

    Shikenan ta dahu,alalan gwangwani yafi saurin dahuwa

  9. 9

    Zakici alalan yanda kike so,da manja ko kuma da sause koma kicita hakanan

  10. 10
Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
rannar
Sokoto State

sharhai

Similar Recipes