Egg Roll💞

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2 yawan abinchi
  1. Flour komi biyu
  2. Sukari cokali abinci daya
  3. Gishiri cokali shayi daya
  4. 5Dafaffen kwai guda
  5. Man suya mai dan yawa
  6. Bakar hoda cokali shayi Rabi
  7. Bota cokali abinci biyu
  8. 25 gMadara gari
  9. Ruwa dai dai Bukat

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki tankade fulawa,ki hadata da sauran busasun kayan gishiri,bakar hoda,sukari da bota kiya ta mutsikawa har sai botar ta ratsa fulawar.sai ki hada madara da ruwa ki dama sai ki zuba a fulawar ki kwaba kada yayi ruwa ruwa kada yayi tauri kuma.Sai kiyi ta murzashi har tsayin minti 7 a rufe a ageje a gefe ya tsimu.

  2. 2

    Sai ki dako kwan ki bare ki dako fulawa ki kara murzawa sai ki fadada fulawa a tafin hannu sai ki saka kwan a tsakiya sai ki nade/ki dunkule ki lulube kwan da fulawar

  3. 3

    Kisa mai a wuta idan yayi zafi sai ki rage wutar ki saka egg roll a wuta ki soya shi har ya canza launi zuwa ruwan kasa(brown) Ana iya ci da shayi,lemo.Aci lapia.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Bint Ahmad
Bint Ahmad @Bint92
rannar
Sallari,Kano Nigeria.
For me,the kitchen is the most special room in the house.Its a place for adventure -not drudgrey,but discovery,sharing and showing off with friend's,trying new ideas.♡☆
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes