Tura

Kayan aiki

  1. Semovita leda daya
  2. Ruwa kofi uku
  3. Yeast
  4. Sugar
  5. Albasa
  6. Mai
  7. Dafaffiyar shinkafan tuwo ko normal farin shinkafa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko uwar gida zaki zuba semo a bokitin da zaki kwaba

  2. 2

    Sannan ki zuba yeast da ruwa ki kwaba dai dai yadda kwabin masan shinkafa yake

  3. 3

    Sannan ki rufe kisa aguri Mai dumi ko Rana yatashi

  4. 4

    Idan ya tashi ki zuba sugar Dan madai dai ci ki yayyanka albasa kanana aciki sannan kisa dafaffiyar shinkafan ki gauraya dakyau idan Kinga yyi kauri sosai Zaki iya Kara ruwa

  5. 5

    Sannan ki gauraya ta ko Ina

  6. 6

    Ki daura kaskon suyan masanki kisa Mai sannan kifara soyawa yadda ake suyan masan shinkafa

  7. 7

    Shikenan MASAN SEMOVITA ki ya gamu
    Kamar haka

  8. 8

    Anaci da sugar,miyar ganye,miyar stew,sannan Kuma anaci haka kawai

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
HAJJA-ZEE Kitchen
HAJJA-ZEE Kitchen @hajjazee3657
rannar
I really love cooking,baking and more 🥰😍
Kara karantawa

sharhai (2)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Ay masar semo tayi ga dadi ga saukin yi 😋😋😋 @
(an gyara)

Similar Recipes