Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Farar shinkafa
  2. Baking powder
  3. Yeast
  4. Attarugu
  5. Albasa
  6. Sugar
  7. Gishiri
  8. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko Zaki tsince farar shinkafarki kiwanketa saiki jikata kibarta kmr tsawon awa daya koh rabin awa saiki sake wanke ta.

  2. 2

    Daganan idan kinada gayan tuwon shinkafa saiki yanka aciki idan babu saiki dafa shinkafa kizuba aciki saiki bada markade.

  3. 3

    Bayan ankawo miki markade saiki zuba yeast,baking powder kisa sugar kisa gishiri kadan kadan saikisa attarugu da Albasa wanda kika jajjaga kijuya saiki rufe kibari yafara tashi

  4. 4

    Bayan yatashi saiki dora tanda akan wuta kisa mai saiki zuba kwabin kibarshi yasoyu shikenan.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Habiba Dauda Ibrahim
Habiba Dauda Ibrahim @habibadaudaibrahim
rannar

Similar Recipes