Kunun shinkafa Ko basisai

HYF Cakes and more
HYF Cakes and more @HYFCakes

#CDF abincin arewacin nigeriya.

Tura

Kayan aiki

30 mins
6 yawan abinchi
  1. Shinkafa (white rice)
  2. Markadadden gyada,
  3. Sukari
  4. lemon tsami kokuma tsamiya,
  5. Madara optional
  6. Ku nun gyada ko kuma kunun basisai

Umarnin dafa abinci

30 mins
  1. 1

    Kidaura ruwanki akan wuta,sai ki wanke shinkafarki,idan ruwan ya tafasa,sai kizuba shinkafar ki,ki jujjuya da ludayi.

  2. 2

    Bayan nan, sai ki dama markadadden gyadarki (groundnut paste) da kauri,karki sa masa ruwa yayi yawa,sai ki taceshi da rariya mai duhu/laushi.

  3. 3

    Idan shinkafarki tanuna halfdone,karki bari yanuna sosai,Sai ki zuba ruwan markadadden gyadar ki,ki jujjuya sosai continuously, har sai ta sake tafasa for about 5 to 8mins.

  4. 4

    Uwargida idan kinaso sai kisa sugar a wannan lokacin,in kuma ba kyaso
    saiki bari.

  5. 5

    Sai kikashe wuta,ko ki sauke,kibarshi yayi sanyi, ko ki fifita kunun sosai, bayan ya yafara hucewa sai ki sa tsamiyar ki ko lemun tsami (lime) sai ki jujjuya.
    Ananne kununki zaiyi kauri kuma zaiyi fari tas.

  6. 6

    Sai kuma idan kina so zaki i ya sa madarar ki,(optional) in Kuma bakyaso hakama ya wadatar. A wanna lokaci idan bakisa sugar daga farkoba zaki iya sa wa.

  7. 7

    Note
    Dalilin dayasa nace za a bar kunun sai yayi sanyi ko temperature shi sai ya ragu sosai kamin asa lemu/tsamiya shine dayawa kunun danyan shinkafa yana guntsari, zakiga yayi tumbubi tumbubi ko yayi separating wa'ansuma sai sun daure da akamu ko cornflour.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
HYF Cakes and more
rannar
cooking is me because its my passion.
Kara karantawa

Similar Recipes