Kayan aiki

  1. Alkama kwano daya
  2. Nono ko tsamiya
  3. 1Butter
  4. 6 cupSugar
  5. Lemon tsami

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko za'a gyara Alkama a tsince datin,sai awanke ta sabi da wata Alkamar ana samun tabo,sai a baxata a rana ta bushe.

  2. 2

    Bayan ta bushe sai abarxo ta,wasu kuma suna nika ta tai laushi amma na baxa yafi kyau.

  3. 3

    Bayan an barxota idan dasafe za'ai to tun dare za' kwaba.

  4. 4

    Yanda za'a kwaba
    Za'a zuba wannan barzajjiyar alkamar a maxubi sai kawo butter nan asaka amurjeta acikin alkamar,

  5. 5

    Sai a kawo nono ko jikakkiyar tsamiya atata ruwan aciki sai akwaba ahada shi ya hadu sai arufe.

  6. 6

    Bayan ya kwana sai a dauko kwabin nan asashi cikin ledar siga ayita buga shi ana yayyafa ruwan kanwa ana kara bugashi,

  7. 7

    Ko kuma asa aturmi ayi ta bugawa da tabarya har yadu,sau a gutsuro amurxa da hannu ya danyi tsayi in bai karyeba to yayi,in ya karye sai a

  8. 8

    Sai a sake bugawa,bayan ya hadu sai afara gutsura ayi masa nadin Alkaki.

  9. 9

    Sai a dafa siga kamar na dubulan,in dahu sai ajiye agefe,sai dora mai awuta,in yayi zafi sai a fara soya Alkakin amma kar watar tayi yawa sabida cikinsa ya samu ya soyu.

  10. 10

    Bayan ya soyu ana kwashe shi sai azuba shi acikin wannan dafaffen sigan abarshi ya mintuna sai akwashe azuba wanda aka kara soyawa, anfiso ana kwashe shi daga mai sai asashi cikin ruwan siga.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Usaina Musa Haruna
Usaina Musa Haruna @cook_37512388
rannar

sharhai (3)

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
@cook_37512388 thanks for sharing a well detailed recipe and welcome to cookpad

Similar Recipes