Kayan aiki

Awa biyu.
mutane 4 yawan abinchi
  1. Wake gwangwani biyu
  2. Mai rabin kwalba
  3. Tattasai guda biyu
  4. Attarugu guda hudu
  5. Farin Maggi Rabin sachet
  6. Gishiri cokalin shayi daya
  7. Garin bushasshiyar kubewa rabin cokalin shayi

Umarnin dafa abinci

Awa biyu.
  1. 1

    Dafarko za'a jika waken na kamar minti biyu,sai a zuba a turmi a surfa shi,sai a wanke a cire duka hancin waken, a gyara kayan miya,sai a nika.

  2. 2

    A buga kullin sosai yadda zai tashi amman kar yayi ruwa don zai sha mai ko ya kwanta,sai a kawo Maggi,gishiri,da garin kubewar a zuba,a qara bugawa sosai.

  3. 3

    Sai a Dora mai a wuta,asa albasa,in yayi zabi sai ana diban kullin ana zubawa,in bari daya yayi sai a juya dayan barin ma, in yayi sai a kwashe.ga dadi ga ba Shan mai.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ummu Khausar Kitchen
rannar
Kano
girki adon mace ina son girki mussaman namu na gargajiya.
Kara karantawa

Similar Recipes