Kosai Recipe

Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
Zaria

#Kosairecipecontest K'osan manja, ba duka mutane suka sanshi ba, sai dai hak'ik'anin gaskiya yana da dad'i, kuma ga lafiya ajikin Mu, saboda an soyashi da ingantaccen mai,wato"MANJA"

Shiyasa na kawowa Mutane,sabon hanyar yin ingataccen k'osai Mai lafiya,bawai sai dole na mangyad'a kad'ai ba. Dad'in dad'awa wasu yarukan sun sanshi sosai. Shiyasa muma muke yawan yinsa a gidan mu,ki gwada yin k'osan manja,kisha mamaki, wajen dad'i da sanya santi. Gaskiya ina son k'osan manja,ko don ingancinsa.

Kosai Recipe

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

#Kosairecipecontest K'osan manja, ba duka mutane suka sanshi ba, sai dai hak'ik'anin gaskiya yana da dad'i, kuma ga lafiya ajikin Mu, saboda an soyashi da ingantaccen mai,wato"MANJA"

Shiyasa na kawowa Mutane,sabon hanyar yin ingataccen k'osai Mai lafiya,bawai sai dole na mangyad'a kad'ai ba. Dad'in dad'awa wasu yarukan sun sanshi sosai. Shiyasa muma muke yawan yinsa a gidan mu,ki gwada yin k'osan manja,kisha mamaki, wajen dad'i da sanya santi. Gaskiya ina son k'osan manja,ko don ingancinsa.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa d'aya da rabi
Mutane bakwai
  1. Wake kanana gwangwani shida
  2. Waken soya gwangwani biyu
  3. Manja na soyawa kwalba d'aya
  4. Maggi fari na cikin sacet
  5. Gishiri domin d'and'ano

Umarnin dafa abinci

Awa d'aya da rabi
  1. 1

    Ga waken da kuma waken soyar,za'a jika waken na tsahon mitoci goma,sannan a tsane,a surfa,a wanke tas! I fidda dusar.Sai a dauko waken suyar ahad'a da waken. A kula shi waken soyar ba'a jik'awa a fidda hancin,sai dai a wanke ahada cikin waken. Gashi kamar yadda kuke gani a hotunan.

  2. 2

    Daga nan,sai a nik'a,kada yayi laushi sosai, saboda yayi ruk'us-ruk'us.Daga nan, sai a zuba farin Maggi da gishiri, kamar yadda kuke gani cikin hotunan.

  3. 3

    Daga nan sai a buga sosai,su had'e

  4. 4

    Sai a d'ora manja a wuta, idan yayi zafi, a saka kullun cikin manjar da cokali ko ludayi K'arami.kamar haka

  5. 5

    Idan b'arayi d'aya ya soyu,sai a juya d'ayan b'arayin Shima ya soyu,kamar haka

  6. 6

    Daga nan sai a,tsame daga cikin maI, da matsami,kamar haka

  7. 7

    Ga sakamakon k'osan manjar Mu, kamar haka.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Salwise's Kitchen
Salwise's Kitchen @cook_16516066
rannar
Zaria
I was born and bred up in Zaria
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes