Kayan aiki

4mintuna
1 mudu
  1. 1Flour mudu
  2. Butter 250g / Simas 1
  3. 2Sugar kofi
  4. Baking powder chokali 1
  5. 3Kwai
  6. Milk Flavor chokali 1
  7. Gishiri chokali qarami 1
  8. Mai kwalba 1 da rabi
  9. Butter scotch da condense milk flavor chokali 1 kowane

Umarnin dafa abinci

4mintuna
  1. 1

    Ki tan kade flour ki cire kofi daya saboda sakawa wurin mulka

  2. 2

    Sannan ki fara hada sugar cikin flour

  3. 3

    Sannan kisa gishiri baking powder da madara

  4. 4

    Se ki hade sannan kisa butter

  5. 5

    Ki saka kwai

  6. 6

    Sanan kisa ruwa kadan kadan

  7. 7

    Kiyita mulka har ya dena laqewa ga hannun ki

  8. 8

    Idan ya mulku Se ki kama murzawada rolling pin ko mucchiya

  9. 9

    Gurin yanka zaki iya amfani da abu 3 zuwa 4

  10. 10

    Na farko pizza cutter sannan almakashi ko marfin kwalba sannan zaki iya saka hannu ki mumula ki gunta

  11. 11

    Ki aza mai bisa wuta yayi zafi gara kiyi amfani da mai wanda baki taba amfani dashi wurin suya

  12. 12

    Ki zuba kadan kadan kinayi kina motsawa don baa barin shi bisa wuta

  13. 13

    Motsawa zesa kada ya dahu wani wuri wani beyi ba

  14. 14

    To fa ga cin cin don sama yara makaranta ko tarbon baki

  15. 15

    Shikuma wantda akeyi da marfin kwalba ga yanda zakiyi nan

  16. 16

    Amma gaskiya kyau ne da shi akwai wuya da bata lokachi gara idan kadan kawai zakiyi

  17. 17

    Ga yawan mai da ya rage seda ya kwanta nayi amfani dashi wurin miya.

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Wanda aka rubuta daga

Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes