Sauce

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Abuja

Wato shi wannan sauce din ba a cewa komai sai hamdala ya kunshi Kayan dadi ba kadan ba. Dan Allah ku gwada ku ban labari. Yanzu na gama nawa da zafinta wlh kowa bismillah

Sauce

Wato shi wannan sauce din ba a cewa komai sai hamdala ya kunshi Kayan dadi ba kadan ba. Dan Allah ku gwada ku ban labari. Yanzu na gama nawa da zafinta wlh kowa bismillah

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti talatin
Mutane uku
  1. Kifi duk wadda ake bukata nayi anfani da panka da banda
  2. Ganda/Pomo
  3. Kwai iya bukata
  4. Albasa manya
  5. Iru daddawan yarbawa
  6. Ginger
  7. Mai ko manja dan daidai
  8. Nama idan ana bukata
  9. Dandano (maggi)
  10. Shombo
  11. Attarugu
  12. Dan fresh tumatir
  13. Ganyen albasa
  14. Nama ko wane iri da ake bukata

Umarnin dafa abinci

Minti talatin
  1. 1

    Da farko zaki jera duk Kayan ankinki a huge daya

  2. 2

    Ki samo pot dinki kisa mai ko manja ko Ki hada duka biyu sai ki zuba albasa dayawa da dan ginger ki soya

  3. 3

    Daga nan sai ki zuba Kayan miyarki da wannan daddawan yarbawan ki soya sama sama

  4. 4

    Sai ki kawo su dandano da kikeso ki zuba akai

  5. 5

    Daga nan sai ki kawo duk proteins dinki ki zuba akai ki juya da kyau sai ki bar miyan yadan soyuwa kadan.

  6. 6

    Zaki dan diga ruwa dan kar ya kama. Kidan barshi na mintuna sai ki kashe. Shikenan kin gama. Sai ki barbada ganyen albasa akai

  7. 7

    Wannan sauce din yana da dadi sosai zaki iya ci da komai, rice,pasta,cous cous, yam etc

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
rannar
Abuja
cooking is my dream and also cooking is all about being creative
Kara karantawa

Similar Recipes