Miyar wake mai dadin gaske

Hamzee's Kitchen
Hamzee's Kitchen @cook_17117332

Wata rana nayi baki ,sai nayi tunanin mai zan musu, sai kawai nace bari nai musu miyar wake, tunda da masu son waken, aiko na tashi nayi musu ,aiko da na gama kan ace me sun cinye, suna santi sai suka tambayen yaya nayi wannan miyar sai ko na fada musu yadda nayi.

Miyar wake mai dadin gaske

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Wata rana nayi baki ,sai nayi tunanin mai zan musu, sai kawai nace bari nai musu miyar wake, tunda da masu son waken, aiko na tashi nayi musu ,aiko da na gama kan ace me sun cinye, suna santi sai suka tambayen yaya nayi wannan miyar sai ko na fada musu yadda nayi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 40 zuwa 4mintuna
wake kofi daya1 yawan abinchi
  1. Abubuwan da ake bukata
  2. Wake,
  3. Tattasai3
  4. Tumatur5
  5. Albasa1
  6. Nama da bushashshen kifi
  7. Mankuli ko manja ludayin miya biyu2
  8. Gishiri ko maggi
  9. 3Attarugu

Umarnin dafa abinci

minti 40 zuwa 4mintuna
  1. 1

    A jika waken a wanke dusar.

  2. 2

    A wanke tattasai da tumatur da attaruhu da albasa a markada.

  3. 3

    A tafasa nama a gyara bushashshen kifi.

  4. 4

    A soya mai a soya kayan miyar a cikin mai a soya nama a zuba a cikinkayan miya.

  5. 5

    A zuba gishiri da maggi da curry da bushashshen kifi a ciki a rufe ya tafasa.

  6. 6

    A zuba ruwan nama a cikin kayan miyar.

  7. 7

    A wanke waken zuba a ciki a bari ya dahu sosai sai yayi laushi da kauri.

  8. 8

    Anaci da dayaffiyar doya ko dayaffiyar shinkafa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hamzee's Kitchen
Hamzee's Kitchen @cook_17117332
rannar

sharhai

Similar Recipes