Oats meh ayaba da dabino

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#sahurrecipecontest.wannan hadin oats na da amfani sosai a jiki mussaman lokacin sahur oats,ayaba da dabino suna kunshe da sinadarin fiber,sugar da sauran sinadarai da suke bawa mutum kuzari ga kosarwa.

Oats meh ayaba da dabino

Masu dafa abinci 3 suna shirin yin wannan

#sahurrecipecontest.wannan hadin oats na da amfani sosai a jiki mussaman lokacin sahur oats,ayaba da dabino suna kunshe da sinadarin fiber,sugar da sauran sinadarai da suke bawa mutum kuzari ga kosarwa.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Oats kofi daya
  2. Ruwa kofi daya da rabi (idan yayi kauri ana iya karawa)
  3. Madara na gari daidai bukata sai a dama da ruwa kadan
  4. Sugar yadda ake bukata
  5. 1Ayaba
  6. 3Dabino guda

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki samu tukunya ki zuba ruwa ya tafaso sai ki zuba oats ki juya ki bashi minti 2 ya nuna idan yayi kauri dayawa kina iya kara ruwa.

  2. 2

    Bayan minti biyu sai ki sauke kisa sugar da madara ki juya sai ki zuba a kofi ki yanka ayaba da dabino ki zuba a kai.ayi sahur lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes