Fate-Faten wake

Chef Uwani.
Chef Uwani. @cook_14144607
Kano State, Nigeria

#kanostate Nutrious food

Tura

Kayan aiki

  1. Wake
  2. Markadaddun kayan miya
  3. Kayan kamshi
  4. Mai
  5. Alayyahu
  6. Nama
  7. Albasa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki markada kayan miya sama sama. Ki zuba a tukunya ki soya shi sama sama da mai. Ki zuba ruwa da Maggi da gishiri ki barshi ya tafasa.

  2. 2

    Ki zuba wankakken wake da kanwa kadan ki barshi yayi ta dahuwa.

  3. 3

    Idan ya kusa dahuwa Sai ki zuba yankakken Albasa dayawa Ki saka curry da tafasashen nama. Ya dahu sosai amma kar ya farfashe. In ya rage Saura minti 3 ki sauke. Se Ki zuba alayyahu.

  4. 4

    Ki sauke. Ki barshi da dan ruwa ruwa. Aci haka ko da bread ko da Jollof. Aci dadi lafia💞

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Chef Uwani.
Chef Uwani. @cook_14144607
rannar
Kano State, Nigeria
Cooking is fun... Homemade is the best...
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes