Whipped cream pudding

Masu dafa abinci 14 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Whipped cream na gari gwangwani daya
  2. Madara ta gari gwangwani daya da rabi
  3. Man gyada chokali biyu
  4. Sugar chokali daya
  5. Fulawa chokali daya
  6. Coco powder chokali hudu
  7. Chocolate flavor murfi daya(optional)
  8. Chocolate brown color murfi daya(optional)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki samu tukunyar ki me kyau ki dora a wuta kisa wutar er kadan,se ki dama whipped cream din da ruwa kofi daya,ki zuba a tukunyar,itama madara ki kwabata da ruwa kofi daya da rabi,ki zuba a cikin tukunyar ki zuba mai,siga,fulawa ma kidan damata da ruwa kadan,se ki ta juyawa,zakiga yayi kauri kamar ruden tuwo.

  2. 2

    To idan yayi daidai kaurin da kikeso se ki sauke,idan kika dena juyawa ze dunqule,dole juyawa zaki tayi,bayan kin sauke se ki rabashi biyu,se ki kwaba coco powder da ruwa dan kadan ki zuba a cikin daya da flavor da color ki juya,se a barshi kaman minti ashirin ya huce.

  3. 3

    Se ki kawo kofi rabi ki zuba fari rabi ki zuba me chakulet,se kisa a fridge ye kaman minti talatin zuwa sama,sanyi ya ratsa shi sosai Se kisha dadi

  4. 4

    Karin bayani,amfanin saka chocolate color saboda ya qarawa pudding din kalar chakuleti sosai,amfanin saka chocolate flavor saboda ya qara yin qanshin chakuleti.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fulanys_kitchen
Fulanys_kitchen @cook_14365493
rannar
sallari qts Kano

sharhai

Similar Recipes