Kayan aiki

  1. Wake
  2. Tarugu
  3. Albasa
  4. Tattasai
  5. Dandano
  6. Sinadaran kamshi
  7. Kori
  8. Gishiri
  9. Dafeffen kwai
  10. Mai
  11. Man ja
  12. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A zuba wake a turmi da ruwa kadan sai a surfa, a cire hancin a wanke shi tas. A saka yankekken albasa, tarugu da tattasai. Sai a markada.

  2. 2

    Bayan an markada sai a saka dandano, mai, gishiri, kori da kayan kamshi a gauraya.

  3. 3

    A samu gwangwani mai tsafta sai a shafe shi da manja, sai a zuba qullin alale a ciki. A samu dafeffen kwai a yanka sala-sala a saka a kowanne daga ciki.

  4. 4

    A zuba ruwa kadan a babban tukunya a daura a wuta, bayan yayi zafi sai a jera gwangwanayen a ciki. Za'a iya saka takarda ko leda a saman kafin a rufe da murfin saboda kada iska ya shiga.

  5. 5

    Idan ya dahu sai a sauqe. Za'a iya cin sa da miya ta musamman ko kuma yaji. Aci dadi lafiya!

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Amma's Confectionery
Amma's Confectionery @ammas_confectionery
rannar
Damaturu, Yobe State
Being creative and trying new recipe is always fun.
Kara karantawa

Similar Recipes