Alalen Gwangwani

Khadija Baita
Khadija Baita @deejaman2020
Kano

Alale abinci ne wanda ake sarrafa shi da wake, ana iya cin shi shishi kadai ko da shinkafa ko da sauce.

Alalen Gwangwani

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Alale abinci ne wanda ake sarrafa shi da wake, ana iya cin shi shishi kadai ko da shinkafa ko da sauce.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake
  2. Manja
  3. Mai
  4. Gishiri
  5. Albasa
  6. Attaruhu
  7. Barkono
  8. Sinadarin dandano
  9. Ruwan dumi
  10. Dafaffen kwai
  11. Kifi ko Sardine da cray fish

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Za'a surfa wake a wanke shi a gyara shi tas duk a fitar da fatar. Sai a yanka albasa, a zuba attaruhu da barkono dai-dai misali a markada tare da waken.

  2. 2

    Da zarar an markada sai a kawo gishiri, sinadarin dandano, da dan spices kadan, a zuba manja da mai kadan, a yanka albasa kanana a zuba, a kawo ruwan dumi a zuba dai-dai misali, baza a saki ruwan da yawa ba, a juya ya hadu sosai.

  3. 3

    Za'a daka cray fish, a gyara kifi a zuba su cikin kullin, za'a iya hadawa da dafaffen kwai a cikin kullin ko kuma bayan an zuba a gwangwani sai a saka Kwan.

  4. 4

    Daman kin tanadi gwangwaneyen ki ki wanke su sun bushe sai a shafe cikin su da man ja a zuba kullin a ciki kamar rabin gwangwanin.

  5. 5

    A jera a cikin steamer ko a kawo tukunya a zuba ruwa a sami wani murfin tukunya da zai shiga ciki sai a jera gwangwaneyen akai a rufe da fai-fai da murfi yadda iska baza ta shiga ba kuma tururin bazai fita ba a dora a wuta ya dahu. Idan ya dahu za'a ga ya cika gwangwanin.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khadija Baita
Khadija Baita @deejaman2020
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes