Homemade Pasta

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

Zaki iyayin pasta dinki a gida a saukake baya wani daukan lokaci da bukatar kayan hadi masu yawa.

Homemade Pasta

Masu dafa abinci 10 suna shirin yin wannan

Zaki iyayin pasta dinki a gida a saukake baya wani daukan lokaci da bukatar kayan hadi masu yawa.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kofi 2 na flawa(da karin kadan na murji)
  2. Kwai guda 3(manya)
  3. chokaliGishiri rabin karamin
  4. Injin taliya(ko wuka idan baki da shi)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki samu roba madaidaiciya seh ki zuba flawa da gishiri ki juya da chokali meh yatsu.sannan kiyi rami a tsakiyar flawar seh ki fasa kwanki ki zuba a tsakiyar flawar cikin ramin da kikayi.seh ki sa chokali meh yatsu ki rika kwabawa da shi har ruwan kwan ya hade da flawar.

  2. 2

    Idan ya hade amma da sauran flawa kadan seh ki juye hadin a kan work surface dinki da sauran flawar seh ki cigaba da murzawa da hannun ki har seh ya hade.idan ya hade seh ki cigaba da murzawa kina kneading har seh ta murzu ta hada jikinta,seh ki sa wuka ki tsaga tsakiyar flawar idan kinga cikin ta yayi sumul ba ramuka toh tayi amma idan da ramuka ki cigaba da murzawa har seh tayi sumul.

  3. 3

    Seh ki sa kwabin a roba ki rufe ki bashi kamar minti 30 sannan ki dakko ki raba gida 4 seh ki dauki guda daya ki fadada shi da hannunki seh ki barbada flawa ki saka shi a cikin injin a lamba daya wurin fadi ki fadada shi,zakiyi haka kamar sau uku sannan ki ninka shi sau uku kamar ninkin wasika seh ki kara saka shi ki fadada sannan ki fara kara lamba kina fadadawa zaki ga tayi falan falan tayi tsawo idan kaurinshi yayi miki seh ki barshi haka.

  4. 4

    Sannan ki raba shi yadda kike son tsawon taliyar ta kasance (kamar inci 12)seh ki saka a wurin da zeh yanka miki a jikin injin din ki yanka.Haka zakiyi da sauran har ki gama.

  5. 5

    Kina iya shanyata a jikin igiyar shanya,ko a buhu ko tabarma meh tsafta ko bayan kujera ya bushe.Idan baki da injin taliya kina iya amfani da wuka meh kaifi ki yayyanka bayan kin murzata kin fadada da rolling pin.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes