Hallaka kwabo

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#ALAWA hallaka kwabo shima nau'in alawa neh na gargajiya,baya wani bukatar kayan hadi dayawa sannan ga dadi da gardin gyada kuma zakin sa dai dai ba meh hawa kai ba

Hallaka kwabo

Masu dafa abinci 12 suna shirin yin wannan

#ALAWA hallaka kwabo shima nau'in alawa neh na gargajiya,baya wani bukatar kayan hadi dayawa sannan ga dadi da gardin gyada kuma zakin sa dai dai ba meh hawa kai ba

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 4Gyada kofi
  2. Sikari kofi 2 da rabi(2 1/2)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki samu gyadar ki ki gyarata ki tsince dattin da marar kyau,seh ki zubata a frying pan ki soyata kina juyata akai akai amma wuta dai dai zaki sa kar ta kone.idan ta soyu idan kin murza da hannu zaki ga bawon na fita seh ki juye a tire ta sha iska.

  2. 2

    Idan ta sha iska ta huce seh ki zuba a turmi ki dan murzata sama sama saboda bawon ya fita seh ki juye a tire ki bakace.seh ki zuba a turmi ki daka amma karyayi laushi sosai ki dan barshi da kura kuran gyadar.

  3. 3

    Seh ki samu tukunya ki dora a wuta ki zuba sikarin ki a ciki,kiyi ta juyawa har ya narke yayi ja amma kar ki barshi ya kone ki sa wutan dan dai dai.Idan sikarin ya narke seh ki zuba gyadar a ciki kiyi ta juyawa da muciya ko chokalin katako har gyadar ta hade da sikarin.

  4. 4

    Seh ki samu tire ki shafa masa mai ki juye gyadar a kai,seh ki samu kwalba ko rolling pin ki fadada shi ko ina yayi level seh ki barshi ya dan sha iska seh ki sa wuka ki yanka ki balla da hannu yadda kike so.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes