Dublan

mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
Kaduna State, Nigeria

#DUBLAN.dublan wani nau'in kayan zaki ne da ake yin shi da flawa a kasar hausa a raba lokacin biki,suna ko sallah.Musamman a biki yana daya daga cikin kayan garan da ake ji da shi,duk a kayan gara nafi son dublan.

Dublan

#DUBLAN.dublan wani nau'in kayan zaki ne da ake yin shi da flawa a kasar hausa a raba lokacin biki,suna ko sallah.Musamman a biki yana daya daga cikin kayan garan da ake ji da shi,duk a kayan gara nafi son dublan.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 1/2 tspyeast
  2. 1 tbspruwan dumi
  3. 1 tbspsikari
  4. 2 tbspbota
  5. 1 tbspmai
  6. 1/4 tspgishiri
  7. 1/2kofi madara
  8. Kofi 2 na flawa
  9. Mai na suya
  10. Kofi 11/2 na sikari
  11. Ruwa kofi1
  12. Ganyen na'a na'a
  13. Yayyan fennel 1/2 karamin chokali
  14. 1/2Lemun tsami
  15. Yayan ridi da habbatussaudah

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki samu roba ki zuba yeast,sugar chokali 1,ruwan dumi chokali 1,bota,mai chokali 1da madara sai ki juya ya hade sosai.Idan ya hade sai ki zuba flawa ki kwaba ya hade jikinshi idan da sauran flawa kina iya yayyafa ruwa kamar chokali 1 ko 2 ki murza ya hade sosai sai ki rufe ki aje shi yayi kamar minti 15.

  2. 2

    Bayan minti 15 sai ki dakko kwabin flawar ki ki kara murzawa sai ki raba gida 3.sai ki dauki daya ki murza shi da fadi sosai kuma yayi falan falan.kafin ki murza ki dan barbada corn flour a kai saboda kar ya dinga mannewa.

  3. 3

    Sai ki samu takardar cardboard ki yanka rectangle shape ki dora akan flawar da kika fadada(saboda dublan dinki suyi girma daya)ki yanka dai dai fadin takardar da wuka ko pizza cutter.sai ki sa pizza cutter dinki ki tsatsaga daga gefe zuwa gefe har sama amma za ki dan bar tazara daga gefe gegen.

  4. 4

    Sai ki samu ruwa ki dangwala a dan yatsan ki ki shafa a duka kusurwa hudun,sai ki ninka shi daga kusurwar sama ki hada da na kasa sai ki manne bakin.sai ki sake shafa ruwa a kusurwa hudun ki sake nunko shi ki shafa ruwa ta cikin gefen ki like shi.sai ki tattare gefen ki manne shi ya dan yi tsawo daya gefen ma ki mishi haka.

  5. 5

    Sai ki bude tsakiyan ta cikin inda kika tsaga ki dakko gefen da kika manne yayi tsawo ki sako shi ta ciki sai ki zazzago shi zai baki shape kamar ganye.Haka zakiyi da sauran kwabin har ki gama.

  6. 6

    Sai ki dora mai a wuta amma kar ki cika wuta,sai ki soya dublan dinki yayi ja sai ki kwashe.yadda zaki hada ruwan sikarin da zaki tsoma dublan din shine,ki zuba sikari kofi daya da rabi cikin tukunya sai ki zuba ruwa kofi daya ki sa ganyen na'a na'a da yayan fennel da lemun tsami rabi ki dora a wuta har sai yayi kauri ya fara danko sai ki kashe ki barshi ya huce.

  7. 7

    Idan ya huce sai ki dakko dublan din kina tsoma shi cikin sikarin ki juya ko ina ya samu sai ki cire ki sa a roba ki sa wasu,haka zakiyi har ki gama.sai ki barbada yayan ridi da habbatussaudah Amfanin na'a na'a da yayan fennel a cikin sikarin zai bashi kamshi mai dadi.kina iya sa habba han(cardamom) ko star annise a maimakon su.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

Similar Recipes