Sinasir da miyar wake

Taste De Excellent
Taste De Excellent @cook_17709533
Kano State

Ina matuqar qaunar sinasir mussaman wannan karon da nayishi d miya ta mussaman abin ba'a magana.

Sinasir da miyar wake

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Ina matuqar qaunar sinasir mussaman wannan karon da nayishi d miya ta mussaman abin ba'a magana.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Danyar shinkafa
  2. Da faffiyar shinkafa
  3. Gishiri
  4. Sugar
  5. Yeast
  6. Man suya
  7. Miyar wake
  8. Wake
  9. gwangwaniTomatir na leda ko
  10. Jajjagagen attaruhu, tattasai, albasa, tafarnuwa da danyar citta
  11. Kayan kamshi
  12. Kayan danadano
  13. Yankakken koren tattasai
  14. Mai
  15. Kifi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki surfa wakenki ki cire dusar tas. Seki sami ruwa ki jiqa waken kamar awa 1 da rabi haka.

  2. 2

    Bayan haka seki tace waken ki qara wankewa kixuba ruwa ki dora a wuta inya dahu sosai xakiga ruwan yayi qasa seki dada ruwa sosai yadda xe miki, sannan ki barshi yayi lugub, seki sa tumatir dinki na leda kadan da jajjagagenki ki barshi yayi 30mins

  3. 3

    Bayan minti talatin seki saka kayan kamshi dana danadano in kinaso ki dansa mai kadan seki sa kifinki da kika cire mai qaya kika maramasa kisa yankakken koren tattasai se ki barshi yayi minti biyar shikenn miyar wakenki tagamu.

  4. 4

    Shikuma na sinasir din xaki jiqa farar shinkafa kamar na tsawon awa daya, bayan awa daya seki dakko ki wankewa kisa dafaffiyar shinkafa ki niqa.

  5. 5

    Seki saka yeast kibarshi y tashi inya tashi seki sa gishiri d sugar sannan ki dora kaskonki a Wuta kina sa mai kadan seki debo hadin shinkafar ki xuba, ki rufeshi ki barshi ya soyu se kicire kisa wani haka xakiyi tayi har ki gama.

  6. 6

    Ba'ajuya sinasir in ana suya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Taste De Excellent
Taste De Excellent @cook_17709533
rannar
Kano State
I'm Aisha Ismail Musa born and brought up in kano, my favorite thing to do at home is to cook
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes