Nannadadden burodi

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

😋

Tura

Kayan aiki

40mintuna
6 yawan abinchi
  1. Burodi mai yanka(yanka 25)
  2. Kilo daya na qirjin kaza
  3. Dafaffen dankalin turawa guda biyar(manya)
  4. Albasa babba daya
  5. Attaruhu(yadda ake son yaji)
  6. Sinadarin dandano
  7. Qaramin cokali na masoro
  8. cokaliCurry qaramin
  9. Kofi biyu na garin burodi
  10. Qwai guda uku

Umarnin dafa abinci

40mintuna
  1. 1

    Da farko za a samu kirjin kaza a yayyanka su kmr akwati(cube),sai a zuba mai a kasko a zuba albasa,in ya fara zafi a zuba kazar ayi ta juyawa har sai ya fara dauko dahuwa,sai fara fitar da ruwa,sai a zuba sinadarin dandano,masoro,curry da wata albasar kadan a qara juyawa da kyau har sai ya dahu

  2. 2

    A wani kwanon daban a 6are dafaffen dankali a gurzashi da abin goga ku6ewa sai a zuba sinadarin dandano,curry da attaruhu,a cakude sai a juye hadin kazar a kai a cakude ya hade jikinshi da kyau

  3. 3

    Burodin mai yanka,za a bi gefe da gefenshi a cire da wuqa,sai ayi amfani da abin murji a kwantar dashi,sai a debo hadin dankali da kazarnan a zuba a kai gefe daya,can daya qarshen a shafa qwai sai a nannadeshi kmr tabarma,sai a dauka a tsumbula cikin ruwan qwai a cire a saka cikin garin burodin ya game jikinshi duka.....haka za ayi tayi har a gama

  4. 4

    Za a iya ajiyeshi a fridge na tsawon kwana biyu kafin a soya,ni wannan nayi ne domin siyarwa ga yadda na shiryashi kafin na miqawa customer

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes