Salad din Couscous

Mamu
Mamu @1981m
Lagos

A gaskiya nakanyima surukata salad din couscous kuma tana sonshi sosai, a kullun nayi, saita tambayeni shin salad din menene wannan? nikuma dadi irin gani chef dinnan saidai nayi murmushi😜yau muna fira nace oh inason shiga gasar couscous amma narasa na mezanyi sai tace yi couscous salad kawai, nace kai ashe kodama kinsan abinda nakeyi😱😱😱😱🤪🤪🤪 shiyasa nayi couscous salad. #couscous.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutum hudu
  1. Rabin ledar couscous
  2. 3Karas
  3. 1Albasa
  4. 3Tumatur madaidaita
  5. 1/2Kokumba
  6. 1Ledar sausage
  7. Sinadaran dandano
  8. Zaitun (idan kana bukata)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga kayan da zanyi salad din couscous nan natanada, na wanke karas, kokumba, albasa, tumatur na yanyanka, haka shima sausage din na yanyanka, couscous kuma na juyeshi a cikin roba, Nakawo ruwa nazuba a tukunya na barshi harya tafasa.

  2. 2

    Nazuba ruwan zafin akan couscous din, sannan natsane ruwan, na ajiyeshi agefe, na dora wata tukunya nasa mangyada nakawo citta da tafarnuwa nasa na soya kadan.

  3. 3

    Nakawo albasa naxuba aciki nayita motsawa har albasar tayi taushi, nakawo couscous naxuba aciki na motse, Alhamdulillah yayi wara wara yadda nakeso, nakawo sinadaran dandano na xuba aciki nacigaba da motsawa, har komi yayi daidai, naxuba mai kadan a wata tukunya, nakawo sausage dina na soyashi shima.

  4. 4

    Nasamu bowl dina naxuba couscous din aciki, nakawo kokumba da karas nasaka aciki, nakawo tumatur da sausage nasa aciki.

  5. 5

    Komi yahadu, wasu suna kara barbada maggi daga baya idan sunaso.

  6. 6

    Haka zalika ana iya zuba man zaitun aciki bayan kagama hada komi, couscous salad ana iyacinshi haka ko kuma aci da abinci. Nagode

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mamu
Mamu @1981m
rannar
Lagos
Eating is necessity but cooking is an Art, i just love cooking
Kara karantawa

Similar Recipes