Fried rice with potato

Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜 @fatumar6855
Zaria City, I'm Married💞💞💞

Wannan girkin yayi santi sosai, oga ya yaba sosai, nasamu yabo

Fried rice with potato

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Wannan girkin yayi santi sosai, oga ya yaba sosai, nasamu yabo

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya
mutum uku
  1. Shinkafa
  2. Kayan miya
  3. Kwai
  4. Irish potatoes
  5. Peas
  6. Green beans
  7. Carrot
  8. Nama
  9. Mai
  10. Kayan kamshi
  11. Sinadaran dandano

Umarnin dafa abinci

Awa daya
  1. 1

    Zakiyi wanke shinkafarki, ki zuba ruwa a wuta, idan ya tausa sai ki zuba shinkafa, sai ki barta yadan dahu kadan, kar ki Bari ta nuna sai ki juye a basket,

  2. 2

    Sai ki daura nama a wuta ki sa spices da albasa da kayan kamshi, ki barta ta dahu sosai tayi laushi.

  3. 3

    Sai ki yayyanka green beans da carrot, da albasa round, nama shina kamar cubes,ki wanke ki ije a gefe.

  4. 4

    Sai ki fere Irish kamar cubes, ki soyashi sama sama, ki fasa kwai ki zuba maggi ki kada sai ki zuba Irish k soyashi duka zaki juye kiyi ta juyawa, barta soyu, sai ki sauke.

  5. 5

    Sai ki daura tukunyarki a wuta ki zuba mai kadan ki soya kayan miyanki, sama sama, ki zuba green beans,carrots peas da albasa, da yankakken namanki, ki juyashi, karki cika wuta, kisa maggi da curry, da Jan onga don kalar.

  6. 6

    Sai ki dauko shinkafarki ki zuba ki juyashi ya hade, sannan ki zuba Irish din a ciki shima ki juya su hade duk.

  7. 7

    Sai ki rage wuta ki barshi kamar minti biyar ko goma sai ki sauke, sai a subama oga ya fara dandanawa😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
rannar
Zaria City, I'm Married💞💞💞
kullum inason koyan abin da ban iya ba, kuma ina son gwadawa🍕🍤🍗🍜🍡🍝
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes