Tuwan semo da miyar ɗanyar kubewa me haɗe da dage dage

Ummu Aayan
Ummu Aayan @Sadiyanahajakitchen
Kano

Ina san tuwo akodayaushe nakan yi lokaci bayan lokaci.nayi wa maman megidana wannan tuwan

Tuwan semo da miyar ɗanyar kubewa me haɗe da dage dage

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Ina san tuwo akodayaushe nakan yi lokaci bayan lokaci.nayi wa maman megidana wannan tuwan

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

40min
4 yawan abinchi
  1. Semovita
  2. Ruwa
  3. Man kuli
  4. Kubewa ɗanya (a wanke ta a goga)
  5. Daddawa (dakakkiya)
  6. Sinadarin dandano da gishiri
  7. Citta,masoro da tafarnuwa(dakakku)
  8. Man ja
  9. Jajjagaggen Attarugu da albasa
  10. Soyayyan kifi

Umarnin dafa abinci

40min
  1. 1

    Ki zuba ruwa a tukunya ki dora a wuta in ya tafasa ki rage wutar kisaka whisker ki tuka garin semo din ki in ya fara kauri kiyi amfani da muciya ki karasa tukawa amma kada yayi tauri sosai se ki zuba man kuli dan kadan sannan ki rufe ya turara kamar minti 4. Seki kuma sa muciya ki tuka sanan ki kwashe

  2. 2

    Ki zuba daddawar ki da dan man kuli da citta, masoro da yar tafarnuwa da dan gishiri sannan ki zuba ruwa da dan yawa ki dora a wuta yayi ta dahuwa. In ruwan ya janye sosai Se ki zuba danyar kubewar da yar kanwa(ungurnu) ki barta minti 3 sannan ki juya ki rufe ta dahu. In ta dahu se ki sauke

  3. 3

    Ki zuba man ja a tukunya ki dora a wuta ki zuba albasa in ta fara soyuwa ki zuba jajjagaggen Attarugu da albasa ki juya minti 3 ki zuba sinadarin dandano da kayan kanshi da dan gishiri ki cigaba da juyawa in ta kusa soyuwa se ki zuba soyayyan kifi. In yayi ki sauke

  4. 4

    Shi kenan se a saka tuwan a faranti Sannan a zuba miyar kubewar se a zuba dage dagen akai. Aci lpia 😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu Aayan
Ummu Aayan @Sadiyanahajakitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes