Mac & cheese

Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617

Abinda yasa wannan girkin yazama special shine gamayyar cheese dakuma hadin nikakken nama mai dadi.

Mac & cheese

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Abinda yasa wannan girkin yazama special shine gamayyar cheese dakuma hadin nikakken nama mai dadi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Dafaffiyar macaroni
  2. Nikakken nama
  3. Kayan kamshi da dandano
  4. Curry
  5. tafarnuwaCitta da
  6. Attaruhu da albasa
  7. Mai
  8. Koren tattasai
  9. Cheese

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko saina fara dafa macaroni dina na ajiye a gefe.

  2. 2

    Sai a dora tukunya a wuta a zuba mai kadan sai a zuba yankakkiyar albasa adan soya na minti biyu. Sai a dauki nikakken nama a zuba, a saka masa kayan kamshi, curry kayan dandano, citta da tafarnuwa, a zuba jajjagagen attaruhu da albasa, sai a soyashi ya dahu kamar na tsohon minti biyar sai a zuba yankakken koran tattasai a barshi yayi minti biyu sai a sauke.

  3. 3

    Zaki goga cheese dinki ki ajiye a gefe. Sai a dauko serving dish a shafeshi da mai sai a dauki macaroni azuba kadan a hawa na farko, sai zuba wannan hadin nikakken nama sai a barbada cheese. Sai a kuma zuba macaroni a hawa na biyu ayi kamar yadda akayi a farko har Agama.

  4. 4

    Sai a sakashi a oven a gasa harsai cheese din ya narke.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617
rannar

sharhai

Similar Recipes