Tuwon Shinkafa Da Miyar Danyar Kubewa

OumHisham
OumHisham @qibdeeya07
Sokoto State

Maigida yana son tuwo da miyar kubewa

Tuwon Shinkafa Da Miyar Danyar Kubewa

Maigida yana son tuwo da miyar kubewa

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya da rabi
Mutane 6 yawan abinchi
  1. Farar shinkafa, Kofi biyar
  2. Ruwa
  3. Miyar kubewa:
  4. Danyar kubewa
  5. Tattasai, tarugu, albasa da tumatur kowanne madaidaici guda biyu
  6. Garin Citta, gyadar miya, daddawa da tafarnuwa babban cokali daya
  7. Dandano
  8. Manja
  9. Nama ko kifi (nidai nayi anfani da nama)

Umarnin dafa abinci

Awa daya da rabi
  1. 1

    Za'a Dora ruwa a tukunya har sai sunyi zafi, sannan a zuba wankakkiya kuma gyararriyar shinkafa a rufe sai a rage wuta

  2. 2

    Bayan minti talatin sai a bufe, Za'a ga shinkafar ta nuna tayi tubus, sai a sanya muciya a tuka, ta tuku sosai sai a barshi kuma ya dan kara sulala sai a kwashe

  3. 3

    Sai hadin miyar kubewa: Za'a gyara dukkanin kayan hadin sai a ajiye su a kusa

  4. 4

    A zuba manja kofi ⅓ a yanka albasa, har sai anji kamshi ya fara tashi alamar yayi, sai a zuba jajjagen attarugu, tattasai, tumatir da albasa a soya a zuba ruwa (a tsayar da ruwan miya)

  5. 5

    Daga nan sai a wanke nama a zuba, a Sanya kayan yaji da daddawa da dandano, da kori (Curry) sai a rufe sai bayan mintina talatin da biyar (idan nama yana da tauri mitinan zasu fi haka) sannan a bude a zuba gogaggiyar kubewa danya

  6. 6

    Sai a bar ta, ta kara mintina ashirin kan wuta, amma kuma Za'a rage wutar sosai

  7. 7

    Bayani: ana iya anfani da murhu biyu domin ayi saurin kammalawa

  8. 8

    Sai a kwashe, aci lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
OumHisham
OumHisham @qibdeeya07
rannar
Sokoto State
Kitchen Crush😄
Kara karantawa

Similar Recipes