Chicken drumstick

#jumaakadai barka da jumaa yan uwa yauma na sake dawowa da wani salon kazae😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki saka chinyoyin kaza a tukunya kisa albasa da Maggi da citta ki tafasa ta har se tayi laushi San nn ki tafasa dankali yayi laushi sekiyi mashing dinshi. Seki dauko kazar ki cire kashinta ki ajiye a gefe seki yanka ta kanana seki juye akan Dankalin kisa jajjagenki ki zuba Maggi da spices ki juya sosai komai ya hade
- 2
Seki wanke hannayenki seki dauko kashin nan ki debo wan nn hadin seki saka akai kiyi shaping dinshi ya dawo kamar normal yadda chinyar kaza take
- 3
Seki barbada masa flour ta rufe shi duka seki fasa egg kisa Maggi da Dan kayan kamshi ki kada seki saka aciki ki juya ko ina ya samu
- 4
Seki saka a bread crumbs seki cire kisa a mai ki soya shi a medium heat
- 5
Shikenan sekiyi serving
Similar Recipes
More Recipes














sharhai