Kunun tsamiya dazai shayar da mutum 100+ domin sadakan Ramadan

Maryama's kitchen
Maryama's kitchen @Maryaaamah_
Kano

A wannan wata mai albarka kowa yanason yayi abunda Allah SWT zai rubanya masa ayukansa na lada, zaka iyayin kunu ko kosai inkanada hali kayi sadaka, duba da halin yau na rayuwa ga lockdown idan kanada dama sai kayi. Ramadan kareem #PAKNIG

Kunun tsamiya dazai shayar da mutum 100+ domin sadakan Ramadan

A wannan wata mai albarka kowa yanason yayi abunda Allah SWT zai rubanya masa ayukansa na lada, zaka iyayin kunu ko kosai inkanada hali kayi sadaka, duba da halin yau na rayuwa ga lockdown idan kanada dama sai kayi. Ramadan kareem #PAKNIG

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

3hrs
100+
  1. Gero kwano 1/1/2
  2. Sugar kwano 1/ 1/4
  3. Dan tsami ludayi 1 na miya,ko tsamiya kwano 1
  4. handfulCitta
  5. Barkono madaidaici
  6. 2farin leda bandir
  7. 20tukunya lamba

Umarnin dafa abinci

3hrs
  1. 1

    Dafarko ga geron nan,zaki auni kwano daya da rabi,ki jikashi overnight ko kuma na tsawon awa 6-8 kafin akai markade,gashinan bayan ya jiku sosai,saiki wankeshi tas

  2. 2

    Ki zuba citta,ki zuba barkono ki kai nika a tabbata anyimiki mai laushi

  3. 3

    Saiki daura tukunya lamba 20,ki zuba ruwa acikinshi kar ya ciko(na zuba bokiti shida,bansan ko liter nawa bane ammade irin medium dinan ne) Saiki rufe ajirashi yatafaso

  4. 4

    Kafin nan ankawo miki nika,saiki zuba ruwa cikin karamin roba ki dan tsinkashi sbda da kauri sosai,to amma bawai ruwa dayawa ba,

  5. 5

    Saiki dauko rariya mai dan laushi bawai laushi lus ba kmr de wnanan,saiki dinga zuba wanan batter din kina tacewa ruwan zakiga kadan kadan ne ke fita amma yanada kauri to haka ake bukata dmaan, idan ruwa ya gama tsanewa saiki juya sauran kullin aciki wata roba,haka zakiyi tayi batare da kin kara ruwa ba sbda idan yayi ruwa bazai kama ba kununki dan mai kaurin dashi za ayi amfani wajen dama kunun

  6. 6

    Bayana kin gama,saiki dawo kan wanda kike zubawa a roba din ki zuba mar ruwa ki tsinkar dashi yayi ruwa ruwa kmr yadda yake a hoto

  7. 7

    Saiki kara tacewa amma wnana karan zaki dinga zuba ruwa kadan kadan har ki gama

  8. 8

    Ga dusan nan saiki matse,hakade zakiyi tayi, ga gasara na mai kauri kitibir ga kuma mai ruwa ruwa, ga ruwan nan yatafasa

  9. 9

    Saiki dauko gasara mai kaurin nan, ki juya shi, saiki sauke ruwan batare da an bude ba,saiki bude kidaga gasarar ki zuba acikin ruwan,saiki dauko ludayi babba da sauri ki juya zakiga yayi kauri sosai

  10. 10

    To anan idan kinada tsamiya zai zmaa daman kin jikashi da ruwa mai dan dumi,saiki tace shi(Sbda lockdown bamusamu tsamiya ba sai mukayi amfani da dan tsami(citric lemon) shima will do) saiki dauko wannan gasara mai ruwa ruwa din zakiga yafara kwantawa saiki dan rageshi kmr rabi haka ahankali zakiga kasan yafi saman dan kauri kadan,saiki zuba ruwan tsamiyanki akai ko dan tsami kamar haka saiki juyashi a matsayin gasara.

  11. 11

    Ki dagashi ki zubashi akai ki juya,kisa sugar shikenan angama

  12. 12

    Sai a kulla, duk leda kopi 1 za a zuba zaibaki kusan 130 insha allah,inkoma ba kullawa zakiyi ba kamar bayarwa zakiyi gida gida zaki zubawa atslt 30-40 family cikin 1ltr bucket each.

  13. 13

    JAN HANKALI wannan hanyar hanyace dazakibi wajen yin kunun tsamiya atake, anayin garin maimakon gasara sai a dama garin a damashi, sannan ba lalllai saikinyi yadda nayiba wajen tacewa zaki iya tsinkashi da ruwa sosai kitace dukka akai daya,saiki bari ya kwanta kmr de gasarar koko(that is atslt yazama 1hr kafin lokacin dazaki damashi) wanna hanyace mafi sauki de., sanan a rashin tsamiya zaki iya amfani da dan tsami zai bada wnanan sour taste din da akeso.

  14. 14

    Gero kwano 1 da rabi =700, sugar kwano daya da kwata =2400, dan tsami =200 barkono=50 citta =150 nika=100 leda manya =200 Icce manya na =200 =4000 naira.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maryama's kitchen
Maryama's kitchen @Maryaaamah_
rannar
Kano
A serial foodie,home cook,food artist,recipe creator, for more of my Recipes check my Instagram page @Maryaaamah_
Kara karantawa

sharhai (12)

Khabeel Muhd
Khabeel Muhd @cook_28962125
Mashallah tnx u so much sis Gskiya naji dadin post dinn

Similar Recipes