Alkubus da miyar alaiyafo

Mrs Maimuna Liman
Mrs Maimuna Liman @cook_13862343
Suleja

Ga dadi ga saukin sarrafawa.

Alkubus da miyar alaiyafo

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Ga dadi ga saukin sarrafawa.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Filawa
  2. Yis
  3. Gishiri
  4. Sikari
  5. Ruwa
  6. Alaiyafo
  7. Attarugu da albasa
  8. Kayan kamshi da sinadarin dandano
  9. Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko za'a tankade filawa a roba,a saka mishi gishiri kadan,sikari kadan sai a gauraye su,a zuba ruwan dumi a kofi a saka mishi yis a ciki sai a gauraya,a zuba acikin wannan filawan ana gauraya shi har kwabin yayi daidai ba ruwa-ruwa ba kuma ba kauri ba,kaman da kwabin fanke, sai a rufe shi da marfi a saka a rana ko waje mai zafi don ya tashi (ma'ana ya kumburo).

  2. 2

    Idan ya kumburo sai a shafa mai a cikin robobi ko gwangwani sai a zuba kullin a ciki,a daura tukunya a kan wuta à saka a ciki sai a daura kwalanda a kai sai a jera robobin a sama a rufe a barshi ya turaru har ya nuna.

  3. 3

    (Miyar kuma) za'a zuba markadadden kayan miya a tukunya,a zuba attarugu da albasa a soyashi da mai kadan sai a saka ruwa daidai sinadarin dandano a barshi ya nuna,idan ya rage ruwan kadan sai a saka yankaken alaiyafo a barshi ya turaru sai a sauke aci da alkubus.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Maimuna Liman
Mrs Maimuna Liman @cook_13862343
rannar
Suleja

sharhai

Similar Recipes