Garau garau da yar miya

Yar Mama
Yar Mama @YarMama
Bauchi

Mai gidan yana son garau garau sosai shiyasa na mishi domin yin suhur.

Garau garau da yar miya

Mai gidan yana son garau garau sosai shiyasa na mishi domin yin suhur.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

60mintuna
2 yawan abinchi
  1. Shinkafa ta gida gwangwani daya da rabi
  2. gwangwaniWake rabin
  3. Kwai guda biyu
  4. Tattasai biyu
  5. Attarugu biyu
  6. Albasa biyu
  7. Dunkule uku
  8. Man gyada cokali biyar
  9. Kayan qamshi na abinci

Umarnin dafa abinci

60mintuna
  1. 1

    Farko na wanke wake na na jika sai na barshi tsawon mintuna 20 sai na daura a wuta ban sa mishi komai ba har ya dahu na tsiyaye nasa a gefe.

  2. 2

    Na gyara shinkafata na tsince duk datti sai na sheka mata ruwan zafi na barta tsawon mintuna uku sai na rege na cire kasa sai na daurata a wuta nasa ruwa ya sha kanta har ta dahu sai na sauke.

  3. 3

    Na gyara su tattasai na na jajjage tare da albasa daya. Na daura tukunya a wuta na sa mai sai na yanka albasa daya a ciki da ya dan soyu kadan sai na zuba jajjge na a ciki sai na mishi hadin su dunkule da kayan kamshi bayan mintuna hudu sai na fasa kwai akai amma ban motsa shi ba saboda bana so kwanduwar ta fashe sai da na lura kwanduwar tayi tauri sannan na juya da daya bangareta nuna sai na sauke. Ni na kirkiro wannan sauce din da kai na don haka sai na sa mata suna(Deeyah sauce).

  4. 4

    Bayan na gama sai na samo plate na zuba shinkafa sai nasa wake sannan na zuba yar miya, shi kenan ya kammala sai ci. Na hada da zobo saboda tayi dadin wucewa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Yar Mama
Yar Mama @YarMama
rannar
Bauchi
Kitchen is my favorite place
Kara karantawa

sharhai (2)

Similar Recipes