Shinkafa da wake (garau garau)

@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
Katsina

Wake da shinkafa wani nau'in abinci ne mai dadin gaske yana da sha'awa dan ni a duk inda na ganshi to baya wuce ni sai naci sanan kuma yanda nake dafa wake da shinkafata idan kika ci dole ki kara kuma ki yaba gwada wanan girki don samun abunda kike so#garaugaraucontest

Shinkafa da wake (garau garau)

Wake da shinkafa wani nau'in abinci ne mai dadin gaske yana da sha'awa dan ni a duk inda na ganshi to baya wuce ni sai naci sanan kuma yanda nake dafa wake da shinkafata idan kika ci dole ki kara kuma ki yaba gwada wanan girki don samun abunda kike so#garaugaraucontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti arba'in
Cin mutum biyu
  1. Shinkafa kofi daya
  2. Wake rabin kofi
  3. Manja kofi daya bisa hudu
  4. (hadin yaji barkono)
  5. Yaji(barkono) kofi daya
  6. D'and'ano (dunkule guda shidda)
  7. Star anise wani kayan kamshi ne kamar tauraro guda biyu
  8. Rabin cokalin Farin magi (d'and'ano)
  9. Kanufari zaa raba cokali kashi hudu ayi amfani da kashi daya
  10. Tafarnuwaguda hudu
  11. Masoro za'a raba cokali gida ukku sai ayi amfani da kashi daya
  12. Kirfa kad'an
  13. (Hadin kayan lambu)
  14. Latas sala sala guda biyar
  15. Tumatur guda biyu
  16. Albasa guda ukku
  17. Kore tattasai daya
  18. Gurji sala sala hudu

Umarnin dafa abinci

Minti arba'in
  1. 1

    Wanan sune kayan da nayi amfani da su gurin girka abincin nan

  2. 2

    Bayan nan na gyara wake na na wanke sa tas sai na daura ruwa a tukunya na zuba shi

  3. 3

    Sai na gyara albasa ta na wanke ta na zuba cikin waken nan amma ban yanka ba uwar gida haka zaki zuba ta guda gudan ta sai na rufe na bashi kamar minti goma zuwa shabiyar

  4. 4

    Bayan nan dana duba naga ya dahu sai na tsame wanan albasar dana zuba ciki wato na fiddata daga cikin waken

  5. 5

    Bayan nan sai na wanke shinkafata na zuba cikin waken da nake dafawa

  6. 6

    Bayan nan saina rufe saida ya fara dahuwa sanan na kawo d'and'ano na na zuba shi guda daya sai na rufe na barta zuwa minti ishirin

  7. 7

    Bayan nan na duba naga tayi sai na tace ta da abun tace shinkafa

  8. 8

    Sai na zuba mai a tukunya koh kasko na yanka albasa na soya shi sama sama

  9. 9

    Sai na dawo ga yaji na na daka shi na fara daka yajin (barkono) sai na zuba d'and'ano na na daka sanan na zuba kayan kamshi na na daka su saida ya daku sanan na kwashe na jera komai a faranti na saka yajin a roba na zuba mai shima a roba bayan ya huce sai na yanka kayan lambu na latas, tumatur,koren tattasai,albasa tare da gurji wanda na wanke su tas nasaka d'and'ano guda biyu(dunkule)

  10. 10
  11. 11
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
rannar
Katsina

sharhai

@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
A gaskia wake da shinkafa akwai matukar dadi wanan girki naji dadinsa sosai sanan kuma mai gida ya yaba da shi uwar gida kema gwada naki don faranta ran mai gida

Similar Recipes