Garau garau

Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
Jigawa State Nigeria

Shinkafa da wake abinci ne da ya shahara a arewacin nigeria #garaugaraucontest

Garau garau

Shinkafa da wake abinci ne da ya shahara a arewacin nigeria #garaugaraucontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa kofi daya da rabi
  2. Wake rabin kofi
  3. Gishiri cokali daya
  4. Maggi star guda biyu
  5. Barkono kofi daya
  6. Mai fari rabin kofi
  7. Albasa guda daya qarama
  8. Kifi danye/soyayye

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara waken ki ki cire masa datti saiki dora ruwa in ya tafasa saiki dauraye waken ki ki zuba

  2. 2

    Daga nan xaki rufe tukunyan ki ki bar waken zuwa minti 40 yayi laushi sai ki tace shi ki juye a matsami

  3. 3

    Zaki dora wani ruwan ya tafasa saiki wanke shinkafar ki ki juye ki barta in ta kusa dahuwa sai ki tace ki hadeta da waken ki maida kan wuta.

  4. 4

    Sai ki rage wutar ki barta a hankali taqara, sai ki sauqe

  5. 5

    Zaki gyara kifin ki in danye ne da lemon tsami ki barshi ya sha iska sai dora mai yayi zafi ki soya shi ki tsame.

  6. 6

    Sannan saiki gyara barkonon ki sa maggi da gishiri ki daka shi sosai, sai ki shirya abincin ki a plate shikenan

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
rannar
Jigawa State Nigeria

sharhai (2)

Similar Recipes