Gurasa

ZeeBDeen
ZeeBDeen @ZeeBDeen

Nayi ta ne a gida kuma tayi dadi sosai

Gurasa

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Nayi ta ne a gida kuma tayi dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

hr 1mintuna
3 yawan abinchi
  1. Fulawa cup 3
  2. Ruwa cup daya da rabi
  3. Gishiri kadan da suga kadan
  4. Sai yeast cokali daya babba
  5. Dakakken kuli kuli
  6. Cabbage, cucumber, tomatoes da albasa
  7. Mai

Umarnin dafa abinci

hr 1mintuna
  1. 1

    Farko zaki hada flour suga gishiri yeast ki juya su sannan ki kawo ruwa ki rika zubawa a hankali kina kwabawa Ana so yayi kamar kwabin panke,, to ruwan in a ga zaiyi yawa sai a rage in kuma yayi kadan a kara sai a rufe kamar minti 15 ya Dan taso

  2. 2

    Sai a kawo kaskon suya a Dora a wuta asa mai kadan in yayi zafi a diba kullun a zuba a buda shi sosai sai yayi tudu Don zaiyi tuwo tuwo a ciki.. In ya gasu a juya haka har a gama

  3. 3

    In an gama sai asa a kwano asa kuli da mai.. A yanka kayan ganyen a zuba.. Zaa iya yanka gurasa itama Don a samu saukin ci

  4. 4

    Shike nan sai a ci

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
ZeeBDeen
ZeeBDeen @ZeeBDeen
rannar

sharhai

Similar Recipes