Hadin dafaffen gero na musamman

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Wannan hadin yanada mutukar dadi da kara lfy. Kana nan yara ma za a iya Basu yana da saurin rike musu ciki.

Hadin dafaffen gero na musamman

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Wannan hadin yanada mutukar dadi da kara lfy. Kana nan yara ma za a iya Basu yana da saurin rike musu ciki.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

25minutes
shan mutum 2 yawan abinchi
  1. Surfaffen gero Rabin kofi
  2. Madara cokali 4
  3. Zuma cokali 4
  4. Kwakwa cokali 6
  5. Vanilla flavor karamin cokali 1
  6. cokaliDakakkiyar citta Rabin karamin

Umarnin dafa abinci

25minutes
  1. 1

    A sami gero a surfa shi a cire dusar. Sai a wanke shi tass. A rege a cire tsakuwar.

  2. 2

    Sannan a dora tukunya akan wuta sai a zuba geron a saka dakakkiyar citta Rabin karamin cokali a zuba wadataccen ruwa Wanda zai dafashi ya yi laushi, Idan ya dahuwa sai a sauke.

  3. 3

    Idan ya dahu za aga yayi kauri ruwan cikin, sai A juye shi a Kofi ko bowl guda 2, sannan a kawo madarar gari kowanne a zuba masa cokali 2, a zuba Zuma da flavour. Sai a kawo kwakwa a watsa akai a juya.

  4. 4

    A sha da duminsa, yanada dadi sosai ga kara lafiya. Kasancewar ya kunshi sinadarai masu Gina jiki. Gero, kwakwa da zuma.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes