Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Doya Rabin guda
  2. 6Kwai
  3. Mai
  4. 4Magi
  5. 4Tarugu
  6. 1Albasa
  7. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki yanka doyarki falefale,sai ki Fere ta ki wanke,sai ki saka ta acikin tukunya ki saka ruwa da gishiri ki dafata.

  2. 2

    Idan ta dafu sai ki tsane ta a kwando ki barta tasha iska.

  3. 3

    Sai ki fasa kwanki ki saka magi da yankakkiyar Albasa da tarugu,sai ki dauko doyarki ki yayyankata yadda kikeso

  4. 4

    Ki aza tasar soya akan wuta ki zuba mai yayi zafi,sai ki dauko doyarki ki saka ta acikin hadin kwanki sai ki saka a mai ki soya.

  5. 5

    Haka zakiyi har kigama da doyarki gaba daya.zaki iya cin soyayyar doya da kwai tareda shayi ko lemu.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima muh'd bello
Fatima muh'd bello @bakerstreat
rannar
Sokoto
cooking is my passion
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes