Dan Malelen tsaki

mum afee's kitchen
mum afee's kitchen @cook_17411383

Gaskia kirkin Yana da sauki sosai ga dadi kuma😋 mum afee's kitchen

Dan Malelen tsaki

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Gaskia kirkin Yana da sauki sosai ga dadi kuma😋 mum afee's kitchen

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

15mintuna
2 yawan abinchi
  1. Tsakin masara kofi daya
  2. Ruwa kofi daya da rabi
  3. Sinadarin dandano 2,manja,salad,albasa,cucumber,tomato &yaji

Umarnin dafa abinci

15mintuna
  1. 1

    Dafarko za'a dura ruwan zafi akan wuta dai dai yadda zai isa,sannan a dauko tsakin masarar nan a wake sa

  2. 2

    Daganan Daman ruwan zafin da aka dura Ya tafasa sai a dauko tsakin masarar da aka wanke,a nemi muciya a dunka juyawa ana zuba Wannan tsakin hakan zaisa ya fara kauri kadan

  3. 3

    Idan yayi kauri sai a rufe a barsa Dan tsakin yayi laushi sai a sauke sa

  4. 4

    Adauko manja a dura a zuba albasa idan ya soyu sai a sauke a nemi faranti a zuba Daman a baya an yanka salad,cucumber,tomato da albasa an kuma wake su sosai da gishiri domin fitar da dattin ganye

  5. 5

    Idan aka zuba a faranti sai a dauko manja a zuba da Sinadarin dandano a dauko yaji da hadin kayan ganyen ka a zuba akai

  6. 6

    Shikenan sai aci yarage

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mum afee's kitchen
mum afee's kitchen @cook_17411383
rannar

sharhai

Similar Recipes